KASASHEN WAJE: An bukaci a fara kiran sallah ta WhatsApp a Ghana

Daga Sulaiman Umar Al'ummar Musulmi a Ghana sun yi watsi da shawarar da aka bayar na cewa limamai su rinka kiran sallah ta manhajar Whatsapp, inda suka ce abu ne da ba za su taba yarda ba. Rahotan dai ya biyo bayan kiran da ministan muhalli, kimiyya da fasaha, Farfesa Frimpong Boateng, ya yi cewa ya kamata limamai su ajiye amfani...

LABARI CIKIN HOTUNA

A nan, Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osibanjo ne a lokacin da ya karbi bakuncin wata tawaga daga Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya wadda akafi sani da WHO a turance a karkashin jagorancin Babban daraktan hukumar, Dakta Tedros Adhanom Ghebreyesus a Abuja.

BARA GURBIN ‘YAN JAM’IYYAR PDP NE KAƊAI KE CANZA SHEƘA ZUWA WASU JAM’IYYU IN JI MAƘARFI

Daga Bishir Sulaiman Tsohon shugaban babbar jam'iyyar adawa ta PDP Sanata Ahmed Maƙarfi, ya bayyana cewa bare gurbin 'yan jam'iyyar ne, da ke ɓata wa jam'iyyar suna, su ne ke fita daga jam'iyyar. fitar irin waɗannan mutane, a jam'iyyar zai bai wa mutanan kirki masu bin doka da oda zama cikin kwanciyar hankali a PDP Ya kuma tabbatar wa da 'yan ƙasar...

Sa6on da PDP keyiwa Allah ne yasa Allah ya karbe mulki ya bawa APC – in ji Bafarawa

Daga Sulaiman Umar Attahiru Bafarawa, tsohon gwamnan Sokoto, ya shawarci 'yan jam'iyyar PDP su kara yawan addu'o'i da tuba ga Allah. A cewar Bafarawa "Laifukan da 'yan jam'iyyar PDP suka yiwa Allah ne yasa yanzu yake azabtar da su a hannun APC. Bafarawa ya yi wannan furuci ne a yayin da yake jawabi a taron Jam'iyyar PDP shiyar arewa maso yamma ranar...

Hon Sani Aliyu Danlami A Bisa Mizani

Daga Abdulrahaman Aliyu Honorable Sani Danlami ya na daga cikin Matasan 'yan siyasa da suka taso da farinjini a wurin jama'a. Tun kafin ya kai bisa wannan kujerar Sani Danlami mutum ne jajirtacce mai akidar siyasa, wanda duk wani wanda ke wakilin Kudu 3 ya san irin gwagwarmayar da ya yi tun a jam'iyyar APP/ANPP har zuwa CPC, kafin ayi maja...

An Kashe Mutane 1,320 A Zamfara

Daga Abdulraman Aliyu Gwamnatin jihar Zamfara ta ce akalla mutane 1,320 ne aka tabbatar sun mutu a shekaru bakwai da barayin shanu suka kwashe suna kai hare-hare kan kauyukan jihar. Gwamnatin jihar ta ce an raunata wasu mutane kusan dubu biyu kuma an lalata gidaje da gonaki fiye da dubu goma. Gwamnatin Tarayyar kasar ta tura runduna sojojin sama zuwa jihar domin...

SIYASAR MU A NAJERIYA

Daga Sulaiman Umar A zaben 2019 in Saraki bai tsaya takarar Shugabancin kasar nan ba zai fuskanci fushi daga Ruhi mai Tsarki - Inji wani malamin addinin kirista Wani babban malami kuma limamin addinin Kirista dake zaune a jihar Legas, Manzo Elijah Ayodele, ya roki shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki,akan ya nemi tsayawa takarar kujera ta shugaban kasa a zaben 2019. Limamin...

An fitar da zakarun da za su Fafata a Gasar Labarai Ta Pleasant Library and Books Da Makarantar Malam Bambadiya

Daga Abdulrahman Aliyu A jiya ne Farfesa Ibrahim Malumfashi ya sanar da fitar da jaddawalin sunaye wadanda za su fafata a. Fitar da na daya zuwa na uku a Gasar. Farfesa ya bayyana cewa. "Kamar yadda aka sanar a ka kuma alkawurta, ga sakamakon gasar da ke kunshe da mutane 15 daga cikin 50 da alkalan gasar suka zaba a matsayin...

Yakin Cacar Baki Tsakanin Sarakuna: Yadda Babangida da Abacha Suka Hambarar da Gwamnatin Buhari a 1985

Daga Abdulrahman Aliyu Fitowa ta daya.. Tun Bayan da aka cire mai martaba Sarkin Gwandu na 19 Alhaji Mustapha Jakolo aka maye gurbinsa da Alhgaji Muhammadu Ilyasu Bashar, wanda aka fi sani da Manjo Janaral Muhammadu Jega, yakin cacar baki ya balla tsakanin Sarakunan biyu, wanda ya haifar da mayar da murtani akan al’ammura da dama da suka shafi masarautar da...