Majalissar Dattawa Ta Ƙasa Ta Ki Amincewa Da Bashin Dala Milliyan 350 Da Jihar Kaduna Ta Nema

Daga Bishir Suleiman S/Kasuwa Dukkan 'yan majalissar dattawa guda uku da suka fito  daga jihar Kaduna basu amince da ciwo wa jihar bashi ba. Kamar yadda gidan talabijin na TVC ya ruwaito a Abuja 'yan majalissar dattawan sun ki amincewa  da buƙatar neman cin bashi da gwamnatin jihar Kaduna ta nema daga asusun Bankin Duniya. Shugaban kwamitin bayar da  lamuni cin bashi...

Na Shiga Aikin Shari’a Ne Domin In Yi Adalcin: Justice Musa Danladi Abubakar

Daga Abdulrahman Aliyu A ranar Lahadi 1/04/2018 ne cibiyar Koyan Sana'o'i ta Marigayi MD Yusuf Karkashin Jagorancin fitaccen Danjarida Malam Danjuma Katsina tare da hadin guiwar wasu masoyan Mai Shari'a Musa Danladi Abubakar suka shirya taron addu'a ga Maisahri'a domin yi masa fatan gamawa lafiya da samun nasara a bisa babban Matsayin da ya samu na zama Alkalin-Alkalai na Jihar...

PDP Ce Ta Talauta Kasar Nan

Daga Abdulrahman Aliyu A Karo Na Biyu, Gwamnatin APC Ta Sake Fidda Sunayen Jiga-jigan PDP Da Suka Wawushe  Dukiyar Nijeriya. Ministan yada labari da al'adu, Alhaji Lai Mohammed ya ce mutane ba su gane dalilin da ya sa ba su saki dukkan sunayen a karo a farko ba, cewa jerin farko somin tabi ne kawai. A karo na biyu sun sake fito...

Ta Shayar Da Mahaifinta Ruwan Nononta Don Kar Ya Mutu

Daga Abdulrahman Aliyu "Da zaran ka kalli wannan hoton dake sama abubuwa da yawa ne zasu zo a zuciyarka, amma da zaran ka san hakikanin labarin sai ka zubda Kwalla a idonka" A daya daga cikin kasashen Turawa ne aka yankewa wani tsoho hukuncin kisa ta hanyar yunwa, in da aka tsare shi a gidan yari da niyyar ba za a...

Mun Kware Wajen Shirya Magudin Zabe, Cewar Sanata Mantu

Daga Abdulrahman Aliyu Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ibrahim Mantu, ya bayyana cewa wannan lokacin na yafiya ne da manta baya tare da tsaya tsayin daka domin maido da martabar Nijeriya. Mantu ya ce yana da hannu cikin magudin zabukan da aka yi a baya. Dan siyasar ya ce "ba dole ne sai na je rumfar zabe na sauya alkaluman...

SINADARIN DASA KAUNA

Abdurrahaman Aliyu 08036954354 Akwai wasu abubuwa da dama masu tasiri a cikin lamuran soyayya,amma ma fi yawan lokuta akan samu cewa 'yan mata ba su fiye bada hankalin su a wannan wajen ba,sukan manta da irin wadannan abubuwansu fake da cewaa ai lallai namiji shi ne mai kashe da rabawa,shi ne ya kamata ya yiwa mace komai,amma ni a hangena...

Fadar Mai Marba Sarkin Katsina Ta Yi Cikar Dango

Daga Abdulrahman A jiya juma’a ne  30 ga Maris 2018 Mai girma Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya halarci nade-naden sarauta da mai martaba Sarkin Katsina ya yi wa wasu fitattun Mutane a Jihar nan. Daga cikin wadanda aka nada din akwai, Kakakin Majalissar Dokokin ta Jihar Katsina Alhaji Abubakar Yahaya Kusada wanda aka nada a matsayin Garkuwan Katsina...

Cin Zarafin Yara Ya Zama Ruwan Dare A Najeriya

Daga Abdulrahman Aliyu A wani bincike da hukumar kula da kananan yara ta duniya ta gabatar a Nijeriya, kan yadda ake cin zarafin kananan yara. Ta bayyana yadda kullum ake samun korafe-korafe na cin zarafin yara ta fuskoki kala-kala. A binciken da ta gabatar ta bayyana cewa a Nijeriya akwai fitattun hanyoyi uku da ake cin zarafin yara, wadanda suka hada...

Jami’an ‘Yansanda Sun Bayyana Wa ‘Yan Jarida Nasarorin Da Suka Samu

Daga Bishir Suleiman S/Kasuwa A ranar laraba ne, rundunar 'Yansandan jihar kwara ta tasa ƙƴeyar waɗanda ake zargi da aikata laifukan tsafi. An kama matsafin da ƙoƙunan kan mutane a garin Ilorin. Kwamishinan 'Ƴansanda Lawal Ado ya bayyana cewa an cafke Sulaiman Adenifuja da ƙoƙunan kan mutane guda uku a kan hanyar Ogbomosho a yankin Eiyekorin dake ilori a ranar...

Ba Bu Wanda Ya Isa Ya Hana Ni Fadar Gaskiya – Dino

Daga Jamil Adamu Balarabe Dan Majalisar dattawan Nijeriya, Sanata Dino Melaye ya ce ba zai yi shiru da bakinsa ba matukar ya ga wani abu da ake gudanarwa a gwamnatin Buhari da bai dace ba. Sanatan ya bayyana wa manema labarai cewa baya tsoron tsage gaskiya a duk inda ta kama a fade ta, ba kuma ya duba daga jam'iyyar da...