Mutun daya ya rasa ransa yayin arangamar da ‘yan hamayya suka yi a Kano

Kano
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano, a ranar Laraba, ta ce mutum daya ya mutu a lokacin da wasu ‘yan hamayya biyu suka yi arangama a Kurnan Asabe da ke karamar hukumar Fagge a jihar. Kwamishinan ‘yan sanda, Mista Hussein Gumel, ya tabbatar wa NAN faruwar lamarin ranar Laraba a Kano. Gumel ya ce rundunar ta tura jami’anta zuwa wajen da lamarin...

Kotu ta yanke wa wani mutum hukuncin bulala 12 a Kaduna

Wata kotun majistare da ke Kaduna, a ranar Laraba, ta ba da umarnin a yi wa wani matashi mai shekaru 26, Yusuf Haruna, bulala 12 saboda ya saci fankar sama guda biyu na sama da Naira 86,000. Haruna, wanda ya amsa laifin nasa, amma ya roki a yi masa sassauci. Alkalin kotun, Ibrahim Emmanuel, yace an sassauta hukuncin ne saboda rokon da...

Gwamnatin Tarayya Zata Horas Da Mata Dubu Biyu Noman Zamani

Gwamnatin Tarayya za ta horas da mata guda dubu 2, Da suka fito daga jihohin Jigawa da Adamawa da Kaduna, Kano da jihar Anambra sai Neja da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja, harkokin da suka shafi noma a zamanance. Ma'aikatar kula da  walwalar  mata,  ta ce, an tsara shirin ne domin tallafa wa kungiyoyin hadin gwiwar mata da su shiga...

Tsohon Gwamnan Bankin Kasa Zai Yi Bukin Kiristimeti Da Sabuwar Shekara A Gidan Gyaran Hali Na Kuje

Tsohon gwamnan babban bankin kasa CBN, Godwin Emefiele, zai yi bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara a gidan gyaran hali na Kuje. Hakan ya faru ne saboda  kasa cika sharuddan bada belinsa da  ya  yi  a  ranar Talata. Bayan zaman kotun a jiya jami’an hukumar gidan  gyaran halin  sun  sake  tafiya  da Emefiele. Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin...

Yawan Bashin Da Ake Bin Najeriya Ya Haura Tiriliyan 87

Yawan bashin da ake bin Najeriya a Kasashen waje zai kai sama da dala biliyan 51 da milyan 759, yayin da a jiya ne shugaban kasa Bola Tinubu ya nemi amincewar majalisar dokoki ta kasa, domin karbo sabon lamunin dala biliyan 8 da milyan 6 da kuma Euro miliyan 100 daga kasashen waje. Bukatar Shugaban kasar wani bangare ne na...

Najeriya Da Angola Sunki Amincewa Da Bukatar Kungiyar OPEC

OPEC
Najeriya da Angola sun ki amincewa da matakin da kungiyar kasashe masu arzikin fitar da man fetur ta duniya Opec ta bukaci su dauka, na rage yawan man da suke hakowa. Rahotonni sun bayyana cewa, kawancen Kasashen da Saudiyya ke jagoranta ba su samu cimma matsaya ba da Angola da Najeriya, wadanda suka nuna  rashin amincewarsu  da  rage yawan man...

Zamu hada karfi da karfe da dukkanin hukumomin tsaro na jihar Katsina – Kwamishina

Ma’aikatar tsaron cikin gida ta jihar Katsina ta jaddada kudirinta na inganta huldar aiki da dukkanin hukumomin tsaro na jihar. Kwamishinan tsaro na cikin gida Dr. Nasiru Mu'azu Danmusa ya bada wannan tabbacin lokacin da ya ziyarci kwanturolan hukumar kwastam ta jihar Katsina. Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan hulda da jama’a na ma’aikatar tsaron cikin gida...

Tinubu ya aika da sako ga majalisar dattawa kan gabatar da kasafin kudin 2024

Shugaban kasa Bola Tinubu ya mika sakon zartaswa ga majalisar dattawa, wanda ke nuni da aniyarsa ta gabatar da kudurin kasafin kudi na shekarar 2024 ga zaman hadin gwiwa na majalisar tarayya a gobe Laraba 29 ga watan Nuwamba da karfe 11 na safe. Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ne ya karanta wasikar niyya ta shugaba Tinubu a zauren majalisar...

Ƴansanda sun hallaka manyan ƴan bindiga uku a Katsina

Rundunar ƴansanda a jihar Katsina ta ce jami’anta sun yi nasarar kashe wasu da ake zargin shugabannin ƴan fashin jeji ne guda uku. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ƴansandan jihar, ASP Abubakar Aliyu, ya fitar a yau Talata a Katsina. Ya ce lamarin ya faru ne a ranar 25 ga watan Nuwamba...

Kotu ta saka ranar hukunci kan shari’ar dan China da marigayiya Ummita a Kano

Wata babbar kotu a jihar Kano ta sanya ranar ci gaba da sauraran shari'ar dan kasar China, Frank Geng Quarong kan zargin kisan kai. Ana zargin Quarong da kisan budurwarsa mai suna Ummulkusum Sani wacce aka fi sani da Ummita a jihar Kano. Kotun, karkashin jagorancin Mai Shari'a, Aminu Ado Maaji ta sanya 6 ga watan Disamba don ci gaba...