An Kone Sama Da Tan 15 Na Miyagun Kwayoyi A Kano

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya yi kira ga hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, data magance matsalolin cikin gida take kawo mata tarnaki wajen yaki da ta’ammali da miyagun kwayoyi. Gwamnan ya yi wannan roko ne  ta bakin shugaban Ma’aikatansa, Shehu Sagagi a  yayin kona Tan 15 da digo 7 na miyagun kwayoyi da  hukumar...

Hukumar Sufurin Jiragen Sama Na Bincike Kan Batan Hanyar Da Jirgin United Air Ya Yi

Hukumar kula da sufurin jirage sama ta kasa ta fara bincike kan dalilan da suka sa wani jirgin United Nigeriya Samfurin NUA 0506 da ya kamata ya sauka birnin Taraiyya Abuja, amma ya yi batan hanya inda ya sauka birnin Asaba na jihar Delta. Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da  shugaban hukumar Kaftin Musa Nuhu ya fitar...

Yan Bindiga Sun Halaka Jami’an Yansanda Biyu A Jihar Imo

‘Yan bindiga sun harbe wasu jami’an yansanda guda biyu tare da wani Matashi har lahira, a yayin wani hari da suka kai wata Mahadar kan titi dake karamar hukumar Ahiazu Mbaise ta jihar Imo. Maharan sun bude  wuta batare da  kakkautawa ba a lokacin da suka je wurin  da jami’an tsaro ke tsayawa domin bincike ababen hawa. Shaidun gani da ido...

‘Yan Najeriya Sun Kashe Sama Da Tiriliyan 2 A Kiran Waya, Sayen Data Cikin Watanni 9

  Yawan kudin da jama’ar kasar nan suka kashe a bangare kiran waya da kuma siyan Data ya karu da kimanin naira Tiriliyan 2 da bilyan 59 a cikin watanni 9n farko na shekarar da muke ciki. Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa  da kanfanonin sadarwa na MTN Nigeria da Airtel Africa suka fitar. Hakan ya nuna cewar an samu...

ASUU Ta Koka Kan Karancin Malamai A Jami’oi

Jami’oin kasar nan na fama da matsalar karancin Ma’aikata, a yayin da dubban malaman manyan makarantun ke haurawa zuwa kasashen waje domin samun aiki mai gwabi, daidai lokacin da masu yin ritaya a jami’oin ke karuwa. Da dama daga cikin rassan kungiyar malaman jami’oi ta kasa ASUU sun tabbatar da haka ga jaridar Punch, inda suka alakanta matsalar, da yadda...

Gwamnatin Tarayya Zata Karya Farashin Makamashin Gas

Gwamnatin tarayya ta bullo da wani tsari na inganta samar da Mamakashin iskar gas a fadin kasar nan, a wani mataki na magance matsalolin da suka shafi samar da makamashin da ake amfani das hi wajen yin girki. Gwamnatin tarayya ta kafa wani kwamiti wanda aka dorawa alhakin bada shawarwari kan yadda za’a inganta samar da makamashin iskar gas din,...

Kungiyar SERAP Ta Bukaci Bankin Duniya Ya Dena Bawa Jihohin Kasar Nan Bashi

kungiyar nan mai rajin tabbatar da adalci a hukumomi da ma’aikatun gwamnati SERAP, ke yin kira ga bankin duniya da ya dakatar da baiwa jihohin kasar nan 36 lamuni, saboda zargin karkatar da kudaden da suke yi Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mataimakin daraktan kungiyar Kolawole Oluwadare ya fitar a ranar lahadi. Wasikar mai dauke da kwananann...

Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi ta rasa babban sufeto sakamakon hadarin mota

Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi ta rasa babban sufeto sakamakon hadarin mota Sifetan ‘yan sanda ya rasa ransa yayin wani mummunan hatsarin mota da ya afku a jihar Kebbi. Hatsarin ya afku ne yayin da motar jami’an ‘yan sandan ta debo jami’ai masu binciken lafuka a kan hanyar Koko zuwa Jega a jihar. Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, Nafiu Abubakar...

Kasafin kudin 2024: Gwamnatin Katsina ta ware kashi 20% a bangaren ruwa da ilimi – Bello Kagara

Gwamnatin jihar Katsina ta ware kashi 20.35 da kashi 20.13 ga fannin ruwa da ilimi, a kasafin kudin shekarar 2024. Kwamishinan Kasafin Kudi da Tsare Tattalin Arziki, Alhaji Bello Kagara, ne ya bayyana hakan a kasafin kudin shekarar 2024, a yau Litinin a tsohon gidan gwamnatin jihar. In za'a tuna gwamna Dikko Radda ya gabatar da zunzurutun kudi har Naira biliyan...

Za Mu Samar Da Wutar Lantarki MW60 Ko Sola MW50 A Kowace Jiha -Gwamnonin Arewa Maso-Gabas

Taron kungiyar gwamnonin jihohin yankin arewa maso gabashin Nijeriya da ya gudana a Yola fadar jihar Adamawa, sun cimma matsayar samar da wutar lantarki mai karfin MW60 ko samar da wutar sola MW50, a kowace jiha cikin jihohin yankin 6. Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya bayyana haka lokacin da yake karanta sakamakon bayan taron na yini biyu Ranar...