An Sace Sandar Majalisar Dokokin Najeriya
A yau Larabe ne Majalisar dattawan Najeriya ta ce wasu 'yan daba sun shiga zauren majalisar inda suka sace sandar majalisar.
Wata sanarwa da mai magana da yawun majalisar Sanata Aliyu Sabi Abdullahi ya fitar, ta yi zargin cewa 'yan dabar sun shiga majalisar ne karkashin jagorancin Sanata Ovie Omo-Agege, inda suka sace sandar, wadda ita ce alamar da ke...
Za Mu Mikawa Gwamnati Motoci 48 Da Muka Bankado A Sokoto- Kwastam
Hukumar hana fasa-kwauri ta Najeriya Kwastam shiyyar jihar Sokoto ta ce ta kama manyan motocin alfarma har guda 48, inda ta ayyana cewa, idan wanda ya mallakesu bai zo ya bayyana ba cikin kwanaki 30 a gaban hukumar ba, za a mika motocin ga gwamnati.
Hukumar kwastam ta ce motocin da ta kama din kirar jip ne.
A lokacin da babban...
Zaben 2019: Shugaba Buhari Ya Nada Mai Magana Da Yawun Kungiyar Yakin Neman Zabensa
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya zabi mai magana da yawun kungiyar yakin neman zabensa a karo na biyu.
Shugaba Buhari ya zabi lauya Festus Keyamo (SAN) domin ya zamo mai magana da yawunsa a bangaren yakin nema zabensa na shekarar 2019.
Festus ya tabbatar da zabensa da aka yi a shafinsa na twitter a yau talata, inda yace, nan gaba kadan...
WASANNI: Manchester City Ta Lashe Kofin Premier
Kofin Premier na farko ke nan da City ta dauka tun wadanda ta lashe a 2014 da kuma 2012.
Manchester City ta lashe kofin Premier ne da bayan West Bromwich Albion ta doke Manchester United 0-1 a Old Trafford.
Man City ta lashe kofin ne da maki 87, inda ta ba abokiyar hamayyarta Manchester United da ke matsayi na biyu tazarar...
ME YA KAI DAMO DA KARE GIDAN GWAMNATIN KATSINA?
Daga Wakilin Taskar Labarai
A Kwanakin baya aka fara ganin sabon tsari na binciken ababen hawa idan sun zo Shiga ko fita daga gidan gwamnatin Jihar Katsina, abin da ba a ta ba yi ba a baya.
Wannan yasa Taskar Labarai ta fara binciken me ya kawo hakan? Binciken mu daga wata majiya Mai tushe, wadda Bata so a fadi sunanta...
Taron PDP ne ya firgita APC ta tsayar da buhari takara- Sule Lamido
Daga Rahoton BBC
Tsohon gwamnman jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya ce taron da PDP ta yi a jihohin Jigawa da Katsina ne ya firgita jam’iyyar APC har shugabannin jam'iyyar suka roki Shugaba Muhammadu Buhari ya fito ya ayyana cewa zai sake yin takara a karo na biyu.
A wata hira da ya yi da BBC Sule Lamido ya ce :...
An Bukaci Sakatarorin Ilimin Katsina Da Su Guji Harkokin Siyasa
Daga Sulaiman Umar
Gwamna Aminu Bello Masari ya yi kira ga Sakatarorin Ilimi na kananan hukumomi da kada suyi dumudumu cikin harkokin siyasa domin su tsare martaba da darajar aikin su.
Gwamnan ya yi wannan kiran ne a sa'ilin da ya kaddamar da shirin ciyar da yara 'yan makarantar Firamare na jihar.
Gwamna Masari ya jaddada cewa wannan Gwamnatin za ta ci...
Mun amince da kafa sabuwar jami’ar Rundunar Sojoji a Najeriya- Majalisar Ministoci
Daga Sulaiman Umar
A zaman da majalisar ministoci ta yi a jiya a karkashin Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osibanjo, ta amince da kafa wata sabuwar jami'a ta rundunar Sojan Najeriya.
Da yake karin haske kan zaman majalisar, Ministan Ilimi, Adamu Adamu ya ce za a kafa jami'ar ce a garin Biu da ke jihar Borno. A halin yanzu dai, rundunar tana...
KASASHEN WAJE: An bukaci a fara kiran sallah ta WhatsApp a Ghana
Daga Sulaiman Umar
Al'ummar Musulmi a Ghana sun yi watsi da shawarar da aka bayar na cewa limamai su rinka kiran sallah ta manhajar Whatsapp, inda suka ce abu ne da ba za su taba yarda ba.
Rahotan dai ya biyo bayan kiran da ministan muhalli, kimiyya da fasaha, Farfesa Frimpong Boateng, ya yi cewa ya kamata limamai su ajiye amfani...
LABARI CIKIN HOTUNA
A nan, Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osibanjo ne a lokacin da ya karbi bakuncin wata tawaga daga Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya wadda akafi sani da WHO a turance a karkashin jagorancin Babban daraktan hukumar, Dakta Tedros Adhanom Ghebreyesus a Abuja.