RASHIN DA’A A GWAMNATIN MASARI….

0

RASHIN DA’A A GWAMNATIN MASARI….
~~~Zanci Ubanki Zan Gwada Maki ni Cikakkiyar ‘Yar’isaka Ce, Inji Binta Abba Ga Hajiya Ambaru…

Daga Taskar Labarai

Wani musayar kalamai da aka yi tsakanin mai ba gwamnan Katsina shawara a kan ilimin ‘ya ‘ya mata Hajiya Binta Abba da dattijiyuwar ‘yar siyasar nan ta Garin Daura mai suna Hajiya Ambaru Wali. Musayar kalaman wanda aka nada a waya.

Taskar labarai ta tabbatar da sahihancinsa ta nu’urar tantace hoton gaskiya ko bayanan gaskiya a kafofin sadarwar na zamani.

Kamar yadda wakilan Taskar labarai suka ji Hajiya Bintab Abba ce mai baiwa gwamna shawara akan ilmin Mata ta bugawa Hajiya Ambaru waya, cikin kalmomi marasa dadi tana ce mata.

“Hajiya Binta Abba ce ke magana, zan ci ubanki karamar ‘yar iska, tsintaciyar mage maras asali, sai na!ci uwarki, zan zo Daura zan gwada maki ni cikakkiyar ‘yar iska ce”.

Da wasu kalaman da ba su rubutuwa kamar yadda musayar kalaman ta wakana wadda aka dauka.

Hajiya Binta Abba ta kara da cewa, “kina yi wa ‘yan Daura iskanci yadda ki ka ga dama ana kyale ki. banza bakin haure to ni zan zo Daura in maki hankali.

A zantawar ta waya, Hajiya Ambaru ta gwada Dattaku ba ta cewa Binta komai ba, sai ma tambayarta ta rika yi “kin Gama?”

Amma sam ba ta yi mata wata magana maras dadi ba ko mummuna ba ta rike mutuncin ta da dattakunta.

Taskar labarai ta jiyo cewa da da aka fara kamfen a yankin Daura Binta Abba ta je Sandamu, Amma barcin kiyayewar Allah da lamarin ya baci, inda masoya Hajiya Ambaru suka so su wujijjiga ta ta yi ta gudu tana boyewa a bayan manyan ‘yan siyasa wadanda ake ganin mutumcin su da abin ya kai ya kawo ma bayan gwamnan Katsina taje ta boye a filin taro.

See also  Jam'iyyar APC Ta Bukaci Kotun Kararrakin Zabe Tayi Watsi Da Kalubalantar Nasarar Tinubu Daga Ja'iyyun Hamayya 3

Taskar labarai ta jiyo cewa da gwamnan Katsina ya lura in aka tashi taro bai san me zai faru ga Hajia Binta ba sai ya sa aka fitar da ita aka ce ta koma Katsina kar batatta ta faru haka aka fitar da ita da kyar, duk da haka sai da aka keta mata gyale da riga.

Taskar labarai ta yi kokarin jin ta bakin Hajiya Binta taki daukar waya taki kuma amsa sakon da aka tura mata a wayar.

Kokarin Taskar labarai na jin ta bakin Hajiya ambaru, shi ma yaci tura,ta ki daukar taki kuma bada amsa a sakon wayar da aka tura Mata.

Duk ‘yan Daura ba mace ‘yar siyasa Mai mutumci .kamar hajia ambaru tana cikin na hannun daman shugaban kasa Buhari saboda mijinta amininsa ne, kuma a tarihin siyasar ta bata taba yin PDP ba duk wani lamarin da ya shafi mutanen Daura a gwamnati sai In da karfin ta ya kare.

Taskar labarai ta gano hatta sarkin Daura ya fusata da wannan cin fuska da Binta Abba tayi wa halastacciyar ‘ya ga masarautar sa.
__________________________________________________________
Taskar labarai jarida ce da ke da cikakkiyar rijista dake bisa Yanar gizo na www.taskarlabarai.com. da kuma sauran shafukan sada zumunta na Facebook, Instigram, youtube da Twitter da whazzapp a lamba ta 07043777779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here