Rashin tsaro: Gwamnati da Hukumomin tsaro sun gaza – Masari

0

Jaridar Daily Trust Ta Ruwaito Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina ya ce gwamnati da hukumomin tsaro sun gaza wajen tabbatar da tsaron ‘yan Najeriya….

 

Masari, wanda jiharsa na cikin wadanda suka fi fama da matsalar ‘yan bindiga, ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da BBC Hausa.

 

Da yake mayar da martani kan matsalar rashin tsaro da ke addabar kasar nan, musamman yankin Arewa maso Yamma, Masari ya ce, “Jami’an tsaro da mu gwamnati ne jama’a suka dogara wajen kare su, kuma mun kasa yin hakan. Amma idan ka duba musabbabin gazawar an kashe jami’an tsaro da dama. Har zuwa makonni biyu da suka gabata wani kwamishinan ‘yan sanda ya rasa ransa; an kashe sojoji, jami’ai sun rasa rayukansu a kokarinsu na magance rashin tsaro.

See also  Dole Ne Sai ECOWAS Ta Nemi Sahalewar Majalissar Dinkin Duniya Kafin Afkawa Sojojin Nijar Da Yaki - Falana

 

“Rashin tsaro bai shafi jihar Katsina kawai ba, ya shafi kusan kowace jiha a Najeriya da ma wasu makwabtan mu kamar Nijar da Mali su ma suna fama da wannan matsalar.”

 

Sai dai ya ce: “An samu ci gaba ba kamar da ba, amma ba mu kai inda muke so ba kuma muna rokon Allah.”

 

Ya kuma ce Najeriya za ta shawo kan matsalar tabarbarewar tsaro kafin gwamnati mai zuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here