Rikici Tsakanin Hon. Salame da Sheakh Musa Lukuwa: An Nemi Sarkin Musulmi Ya Tsawata Musu.

0

Rikici Tsakanin Hon. Salame da Sheakh Musa Lukuwa: An Nemi Sarkin Musulmi Ya Tsawata Musu.

Rikicin mayar wa da juna bakar magana da cece-kuce da ake yi kwananan tsakanin Hon. Abdullahi Balarabe Salame dan majalisar wakilai na APC dake wakiltar Gwadabawa/illela da Sheakh Musa Ayuba Lukuwa, mutane sun bukaci mahukunta su shiga tsakiyar lamarin domin sasanta su.

Al’ummar jihar Sokoto sun fara hawa saman kafafen yada labarai sun nuna damuwa matuka kan yadda Hon. Salame da Sheakh Musa Lukuwa suka mayar da zagin juna kamar ba’a komai ba.

An dai bukaci mai martaba sarkin musulmi Muhammad Sa’ad Abbakar III, da ya shiga tsakiyar lamarin rikicin domin sulhunta su tun kamin lamarin ya faskara.

Rikicin nasu wanda ya samo asuli ne bayan da shi Sheakh Musa Ayuba Lukuwa ya roki Allah kar ya baiwa Hon. Salame nasarar zama gwamnan Sokoto a 2023 kasancewar a cewar shi, shi Hon. Salame azzalumi ne kuma baya da amfani ga al’ummar yankin sa. Anan ne dai shi kuwa Hon. Abdullahi Balarabe Salame ya mayar da zazzafan martanin kalamai zuwa ga Sheakh Lukuwa abunda ya masa ya kiran yi Sheakh Lukuwa da sunan Mahaukaci, Marar Asuli na Kwarai.

See also  Nelson Mandela ya koyar damu yadda zamu koyar da zaman Lafiya a duniya

Wannan rikicin cacar bakin ya kaure tsawon kwanaki 10 bayan da kowane bangare yake cigaba da sakin zazzafan kalamai zuwa ga junan su dake hatsaniyar.

“A wannan gabar ne ya kamata ace Hon. Salame da Sheakh Lukuwa sun ja layi bayan musayar kalamai da suka yi da suna”

“Sam wannan abun bai kamace ace gari irin birnin mujaddadi dan fodiyo ana irin hakan ba, domin akwai kalamai da suka fara fitowa daga bakunan wadannan mutanen dake kokarin zubar da mutuncin jihar mu a sassan kasar nan”~ inji Al’ummar jihar Sokoto

‘ Ya kama ta ace, mai martaba sarkin musulmi Muhammad Sa’ad Abbakar ya tsawata ya kuma yi burki da wannan rigimar dake iya janyo babbar matsala anan gaba, kawai ace dasu su daina haka nan’ Al’ummar jihar Sokoto sun bukata


Jaridar Sokoto

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here