RIKICIN ZABEN MUSAWA:
……..BAN SAN KOMAI BA
……….In ji Aliyu Abdullahi (Janaral)
Muazu Hassan
@ katsina city news
Mai karatu wannan ita ce hirar da jaridun Katsina City News ta yi da dan takarar kujerar dan Majalisa Wakilai a Musawa da Matazu da aka yi tsakanin Aliyu Abdullahi da Ibrahim D. Murtala da Mamuda lawal , kan rikicin da aka yi wanda ya jawo rasuwar wani matashi da ake kira Abdul Musa, wasu suka jikkata.
A cikin wannan hirar, Aliyu Abdullahi da aka fi sani da Janaral, ya nisanta kansa da rikicin, tare da neman a bar doka ta yi aikinta don a gano tare da hukunta masu hannu a rikicin.
Katsina City News: Me ka sani a kan rikicin zaben Musawa?
Aliyu Abdullahi (Janaral): Babu abin da na sani, sai abin da na ji, da kuma wanda muke jiran jami’an tsaro su fitar da sakamakon binciken su. Tun da sun kama mutane, mutanen da aka kama suna wajen su, kuma sun yi jawabin su. Jami’an tsaro sun kama motocin da aka shigo garin Musawa da su. An san daga inda motocin suka zo, tabbas sun fadi wa ya dauko su haya. Jama’in tsaron sun ji daga mutanen Musawa da Matazu.
Mutanen garin Musawa inda aka yi zaben nan shaida ne, sun shaidi yadda wasu mutane baki a ranar suka zo suka cika masu gari.
Rikicin da aka yi abu ne wanda yake ba ya bukatar wani dogon nazari ko bincike, sai jiran lokaci don in jami’an tsaro sun fitar da sakamakon binciken su da hujjojin da za a iya gabatarwa a gaban shari’a.
Abin da nake so ka sani. Na shigo siyasa ne bisa roko da tilascin mutanen Musawa da Matazu. Na dau lokaci ina ayyukan raya kasa da taimakon al’umma a wannan yankin namu. Kowa ya san wannan. Ginen-ginen rijiyar burtsatse, tallafawa kasuwanci mutane, daukar matasa aiki, da wasu ayyukan. Ban da tallafin kudi ga dai-daiku da kungiyoyi. Ba bu wata mazaba a Musawa da Matazu da banyi ma wani aikin Alheri. Don haka ni ba Bako bane.
Da siyasa ta matso aka fara tilasta mani in zo in yi takara. Sam na ki. Aka yi ta kiraye-kiraye na ki. Sai da manyana a Musawa da Matazu suka fara nuna bacin ransu, sannan na amince bisa sharadi. Sharadin da na bayar daya ne. Duk siyasar da za a yi a yankin in dai a kan zabe na ne ba ni bukatar wani tashin hankali. Kuma aka amince. Da wannan sharadin na shigo takara.
Katsina City News: Wane tabbaci kake da shi za ka iya nasara ko ba bangar siyasa?
Aliyu Abdullahi (Janaral): Na fito daga Musawa, wadda kuri’un mu sun fi na Matazu yawa. Don haka ko kuri’un Musawa kadai na rike zan iya cin zaben.
Balle a Matazu ina da masu kaunata, kuma sun sha alwashin ni za su zaba.
Kuma An je zaben gwamna.kuri un musawa da Matazu baki dayan ta aka ba Dan takara ta .gwagwaren katsina.
Na fada maka a baya, kira da roko na aka yi in yi takarar nan. Dattawa da masu zaben Musawa kaf suna tare da ni. Saboda ni ke tare da su kullum fiye da abokan takara ta. Ya za a yi ni da ke tare da nasara in so a yi fada? Ai mai nasara ba ya son tashin hankali.
Kar ka manta kwana hudu kafin zaben fitar da Dan takara na kewaya kananan hukumomin Matazu da Musawa da motoci kusan dubu da mutane masu tarin yawa akayi taron lafiya aka tashi lafiya.ba fasà mota, ba sata , ba jin ciwo ko gardama mai karfi ba in da akayi.
Katsina City News: Me ya sa aka yi zaben latti ba lokacin da aka tsara ba?
Aliyu Abdullahi (Janaral): Wannan ai bai saba wa duk wata dokar zaben fid da gwani ba. A zaben fid da dan takarar Gwamna a Katsina da safe aka ce za a yi, amma sai dare aka fara, aka kwana a filin zaben.
Duk Katsina ba zaben da aka yi a jam’iyyun nan da aka yi shi kamar yadda aka tsara, sai an samu tasgaron lokaci.
Amsar wannan su masu shirya zaben ne za a tambaya. Amma ka sani ba wani laifin da suka yi.
Katsina City News: Me ke tsakanin ka da sauran ‘yan takarkarin?
Aliyu Abdullahi (Janaral): Ni a wajena babu abin da ke tsakanina da su sai alheri. Wasu ma har da dangantaka ta auratayya ke a tsakanin mu. Muna mutunci, muna zumunci. Ba ni nufi ko fatan komai da su sai alheri. Amma su ban san zuciyarsu ba.
Katsina City News: Wa ya kai ‘yan daba da makamai wajen zaben?
Aliyu Abdullahi (Janaral): Wannan jami’in tsaro za ka tambaya. Da farko dai wadanda suka zo ba ‘yan Musawa ba ne, baki ne. Dokar zabe ta hana kawo ‘yan daba a wajen zabe.
Mutane a garin Musawa sun ga yadda bakin nan da aka gayyato suka rike bace hanya wajen shiga da fita garin. Wannan ya nuna maka hatta wanda ya gayyato su ba dan Musawa ba ne.
Rokon mu shi ne jami’an tsaro su gaggauta fitar da sakamakon binciken su su kai duk wanda ake da zargi kotu, domin kotu ta yi aikin ta a kan sa.
Daga karshe ina ta’aziyya ga iyalan wanda ya rasa ransa. Allah ya jikan shi. Ina sake jajanta wa duk wadanda a ka ji wa ciwo ko aka barnata wa dukiya.
Ina jinjina ga mutanen Musawa da Matazu da suka ki yarda da shiga bangar siyasa, wanda ta sanya sai dai a kira wasu su yi masu banga a gari.
Ina jinjina ga jami’an tsaro da suka dau mataki cikin gaggawa kafin lamarin ya wuce iyaka. Na gode.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245