ROKO GA GWAMNAN KATSINA: A BADa HAYAR GIDAN REDIYON KATSINA

0

ROKO GA GWAMNAN KATSINA: A BADa HAYAR GIDAN REDIYON KATSINA
Daga jaridar taskar labarai
Wasu masana harkar sadarwa, sun roki gwamnan katsina da ya basu hayar gidan rediyon katsina.a wata wasika da suka rubutawa gwamnan katsina kuma taskar labarai ta samu kwafi.
Sunce gidan rediyon yana da muhammaci yana kuma da kwararrun ma aikata wadanda suke da ilmi da gogewa. Amma ya zama kwarangwal.
Babu tabbacin lokacin aikinshi da lokacin hutu.gashi shi kadai ne, tashar AM a katsina mai iya karade duk birni da karkara na jahar.amma Sam ya zama shirim baci ba.
Masanar karkashin kamfanin out reach media concept sun ce suna neman gwamnatin jahar ta basu gidan rediyon, bisa sharadin ta dauke masu hakkin ma aikata kawai.
Amma duk sauran kudin gudanarwa, a barsu zasu nemo su rike gidan rediyon da bude tashar karfe shidda na safe da kuble ta sha daya na dare.da kuma tabbacin kama tashar duk fadin jahar katsina.
Masanan suka ce, zasu samar da kudin rike gidan rediyon su kuma samar da kudin shiga ga gwamnatin jahar.wanda duk wata uku zasu Dora ma kansu abin da zasu ba gwamnatin jaha.a matsayin riba..
Suka ce, shekararu biyun farko gwamnati ta dauke masu Albashi da hakkin ma aikata..amma daga nan a kyale su, zasu rika baya ma kansu Albashi kamar yadda wasu hukumomin keyi, misali KTSTA.waterboard.da revenue board.
Rediyon shine kafar watsa labarai mafi sauki da sauri wajen isar da sako.acikin Al umma.
Masanan suka ce, a wannan lokacin da gwamnatoci ke nemarwa kansu kudin shiga da rage nauyi da fatan gwamnan zai duba takardar su.
Sukace gidan rediyon katsina bai da wata matsala sai matsaloli guda biyu.matsalar mutum daya da rashin kyakykyawan tsari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here