ROKON ALFARMA ZUWA GA MAI GIRMA GWAMNA MASARI.
Daga Ahmad Tijjani Gafai, 08030828093
Mai Girma Gwamna, Muna Neman Alfarmar Tallafin Agajin Gaggawa A Mahaifar Shugaban Hukumar Bada Agajin Gaggawa (SEMA)
Mai Girma Gwamna Unguwar Gafai Dai Ba Ɓoyayyar Unguwa Bace A Gareka, Domin Unguwa Ce Wadda Take Tsakiyar Birnin Katsina, Kuma Sun Bada Gudummuwa Sosai Wajen Kafa Wannan Gwamnati, Duk Kasancewar Ni Babu Ni A Cikin Waɗanda Suka Baka Gudummuwa, Amma Wannan Sako Ne Nake Isarwa Na Al’ummar Wannan Yanki Namu.
Akwai Mashahuran Masoyanka Da Suke A Cikin Wannan Yanki Na Gafai Wakilin Yamma II , Mai Girma Gwamna Ko Don Albarkacin Yan Siyasa Irin Su Babangida Nasamu A Daure A Taimaka Mana Da Hanyoyin Ruwan Da Tafkunan Mu Zasu Rinƙa Fitar Da Ruwa Ba Tare Da Rugujewar Gidajen Mu Ba.
Ya Mai Girma Gwamna Koda Baayi Mana Domin Kuri’ar Da Yan Wannan Yanki Namu Suka Bayar Ba Ya Kamata Ayi Masu Domin Yan Siyasa Irin Su Babangida Nasamu, Domin Shi Ɗin Tsohon Kansila Ne A Wannan Yanki Namu, Haka Kuma Yayi Dan Majalisar Jiha Shekara Takwas Haka Kuma Ya Riƙe Shugaban Hukumar Sufuri, Bugu Da Ƙari Kuma Yanzun Shine Shugaban Hukumar Bada Agajin Gaggawa (SEMA).
Mai Girma Gwamna Kusan Tafkuna Guda Biyar Muke Fama Dasu A Wannan Yanki Namu Waɗanda Suke Ambaliyar Ruwa Duk Shekara Makwabtan Waɗannan Tafkunan Suna Shiga Ƙunci Sakamakon Ambaliyar Ruwa, Mai Girma Gwamna Wannan Shine Jerin Sunayen Tafkunan.
1. Tafkin Bakin Gida.
2. Tafkin Janwake.
3. Tafkin Alh Muaruf.
4. Tafkin Sha Ruwa.
5. Tafkin Faskare Wanda Yake A Bayan Gidanda Aka Haifi Hon. Babangida Nasamu.
Duk Waɗannan Tafkunan Wallahi Suna Bukatar Agajin Gaggawa, Don Allah A Taimaka Masu A Duba Koken Mu.