Rundunar sojan Sahel sanity sun damke wasu dillalan makamai

0

Rundunar sojan Sahel sanity sun damke wasu dillalan makamai su you —- kanal Aminu Iliyasu

Daga shu’aibu Ibrahim Gusau

An bayyana cewa dakarun rundunar Sojojin Operation SAHEL SANITY dake kula da karamar hukumar sabon Birni ta Jihar Sokoto sun sami nasarar damke wasu dillalan miyagun makamai su uku a shiyyar Dantudu dake Lardin Mailailai a cikin Karamar hukumar Sabon Birni ta Jihar Sokoto.

Hakan ya fitone cikin wata takarda mai dauke da sa hannun, mai kula da harkar yada labarai na rundunar sojoji, Kanal Aminu Iliyasu ,ya Kara da cewa cikin wadanda aka Kama akwai Alhaji Adamu Alhassan da Salisu Adamu da Abdullahi Sani.

Ya ce dukkanninsu yan asalin kasar Niger ne, ya ce Dakarun Sojojin sun sami nasarar datse wadannan masu safarar miyagun makamai ne bisa ga bayanan sirri inda suka samesu da bindigu kirar AK 47 guda 6 tare da gidan harsasai na bindigar AK 47 guda uku gami da alburusai samfirin 7.62 mm Special guda 2, 415, boye a lunguna dabam dabam a cikin motarsu.

See also  YAN TA ADDA SUN KAI HARI GARURUWA UKU DARE DAYA A BATSARI JAHAR

Ya Kara da cewa binciken farko ya nuna cewa waddanan miyagun makamai dai na kan hanyarsu ta zuwa hannun wasu yan bindiga ne dake karamar hukunar Isah ta Jihar Sokoto , inda amfani da su na iya jawo halaka ga dubban jama’a da basu jiba basu gani ba.

Iliyasu ya ci gaba da cewa cikin wadanda aka kama, cikin masu laifin, Alhaji Adamu Alhassan wanda aka gano cewa yana dauke da cutar suga ya suma, wanda kuma ya rasu daga karshe yayin kokarin gaggauta kaishi asibiti.

Ya ce duk da haka an ci gaba da binciken sauran abokan illarsa guda biyu domin a bi diddigi wajen kama duk wani mai hannu cikin safarar wannan miyagun makamai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here