sake maka gwamna Ganduje a kotu

0

WATA DABAN: An sake maka gwamna Ganduje a kotu

Masu naɗa saraki a masarautar Kano sun sake kai gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje da majalisar dokokin jihar ƙara gaban kotu, Inda suke ƙalubantar kafa sabuwar dokar kafa masarautu ta 2019 bayan rushe tsohuwar da kotu tayi.

Suna zargin cewa a wannan karon ma ba’a bi doka wajen samar da masarautun ba, domin kuwa an samar dasu ne duk da umarnin wata kotu da ya hana yin hakan.

Tuni kotun ta sanya ranar 17 ga watan nan domin fara sauraron karar.

See also  WANE LAIFI DASUKI YAYI WA BUHARI?

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here