Sako Zuwa Ga Masoyiya Ta Kuma Abar Kaunata Ummi Rahab.

0

Sako Zuwa Ga Masoyiya Ta Kuma Abar Kaunata Ummi Rahab.

Hakika tun lokacin da na fara tozali dake cikin fina finai na shiga matsananciyar damuwa ayyukana sun tsaya cak.

Na tsunduma cikin bakin duhu bansan yadda zanyi na fitar da kaina ba, rayuwata tana cikin hadari har zazzabi nake yi saboda ke.

Ummi Rahab ki taimaka ki agazamin ki ceto rayuwata daga kogin soyayyarki, in cikin wadanda basa son mata ‘yan film Amman Allah ya jarrabeni da kaunarki bansa yadda akayi na fada kogin sonki ba.

Ni ba mai dukiya bane ba dan kasuwa bane, dan Jarida ne ni kuma dalibi ne,

See also  Labarin Soyayyar Laila Da Majnun .Daga Salahudden Uthman Idris

Dalilin fitar da wannan rubutun shine nasan wannan hanyar da na biyo ita ce kawai zata saka sakona ya isa gare ki, bana son na bar soyayyarki a zuciyata gashi bansan inda zan ganki ba.

Indan sakona ya isa gareki ki taimaka ki agaza ki karbi tayin Soyayya ta, kiyi jihadi domin ceton ruhina.

Daga Masoyinki
Comr. Umar Abdullahi Zango

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here