SAMIR ISMAIL MUSAWA YA ZAMA “AMBASADA” na kungiyar international model United nations

0

SAMIR ISMAIL MUSAWA YA ZAMA “AMBASADA” na kungiyar international model United nations
Daga Zainab Ahmad
@ katsina city news.
Wata kungiya mai hadin gwaiwa da hukumar majalisar dinkin duniya mai suna “international model United nations’. ta baiwa Samir Ismail musawa matsayin “campus ambassador”
Kungiyar mai aiki kafada da kafada tare da hukumomin majalisar dinkin duniya na “UNDP” hukumar majalisar dinkin duniya mai kula da raya kasashe.da hukumar “UNHCR” hukumar majalisar dinkin duniya mai kula da yan gudun hijira da wadanda yaki ya kora daga muhallansu.
Da kuma hukumar “UNESCO” wadda ke kula da ayyukan musamman na majalisar dinkin duniya.
Samir Ismail musawa ya samu horo na musamman daga wannan kungiyar tsakanin watannin July da kuma agusta na 2021, kafin tabbatar masa da wannan matsayin na “Campus ambassador ”
Samir ismail,shine matashin mai shekarunshi da ya taba kai wannan matsayin a wannan kungiyar a arewa maso yamma a Najeriya.
A shekarun baya, matasa daga kudancin kasar nan ne ka hawa wannan muhimmin mataki.
Da wannan matsayin, Samir yanzu ya zama muhimmin mutum a kasar nan Wanda wannan kungiyar ke kallo.
Babbar hedkwatar kungiyar yana birnin new York ta amurka mazaunin majalisar dinkin duniya. Suna kuma da ofishin tuntuba anan Najeriya.
Kwanakin baya ma wata cibiyar kwararrun masana akan sha anin mulki ta kasa sun baiwa Samir Ismail Musawa matsayin dakta na girmamawa “DR”
Suka amince masa, in yana bukata yana iya rika kara sunan dakt a a sunan shi. Wannan ne Dalilin da ya Sanya a sunan sa yake rubuta DR Samir Ismail musawa.
Alhaji Samir shine shugaban rukunin kamfanin ASI Musawa and brothers petroleum Nigerian Ltd.da kuma sanyinna global.

See also  KUDI SUN RABA KAN YAN FIM A KATSINA


@ jaridar taskar labarai
Www.jaridartaskarlabarai.com
Katsina city news
Www.katsinacitynews.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here