SANARWA TA MUSAMMAN
A yau laraba 14/8/2019 shugaban kasa Muhammadu Buhari GCFR ya kai ma ‘yan gudun hijra dake karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina ziyarar jaje da ganin halin da suke a ciki.
Mu a jaridar Taskar Labarai mun fi kowa farin ciki da wannan ziyarar don ziyarar nasara ce daga ciki nasarorin aikinmu na jarida kuma babbar nasara ce da jaridar ta samu wanda bai taba gushewa ba a tarihi.
Jaridar Taskar labarai ta fara bayyana halin da mutanen Batsari ke ciki na hare-haren barayin dajin Rugu. Ta dau lokaci tana bada rahoton da hotuna a shafukanta na yanar gizo da sauran zaurukan sada zumunta.
Daga nan, wasu jaridun suka rika amfani da rahoton ta da kuma hotunan ta, wannan ya jawo duk hankalin kafofin watsa labarai ya karkata ga abinda ke faruwa a Batsari.
Jaridar ta dau wakilan wucin gadi a yankin wanda hari na afkuwa zasu sanar dashi kuma nan da nan zasu saka hotuna.
A watan satumba na 2018 jaridar ta fitar da wata takardar manema labarai wanda ta jawo hankalin shugabannin kasar nan halin da hare-haren Batsari ke ciki, kafofin watsa labarai da yawa sun yi amfani da wannan sanarwar manema labaran cikinsu har da biyu na kasashen waje.
A lokacin zaben 2019 jami’an jaridar sun jagoranci ‘yan sa ido na kasashen waje suka je yankin na Batsari suka ga halin da ‘yan gudun hijirar ke ciki da yadda suka yi zaben.
Muna godiya ga Allah wannan dan karamin aikin namu yayi tasirin da yanzu hankalin duniya ya karkata cewa mutanen Batsari na cikin ukubar mahara.
Taskar labarai zata fada rahotonninta zuwa yankunan Danmusa da Kankara, musamman Kankara wadanda sun riga Batsari shiga wannan halin amma ba a sani ba.
Taskar labarai zata yi tsari irin Wanda tayi a yankin Batsari, rahotannin zasu rika fita Hausa da tTranci a Taska da kuma ‘yar uwarta The links news.
Mun gode
Muhammad Danjuma
A madadin jaridun Taskar Labarai da The Links News