SANATA AHMAD BABBA KAITA ZAI KOMA PDP?
Muazu Hassan
@Katsina City News
Rahotonni masu inganci na nuna yiyuwar Sanata Ahmad Babba Kaita zai canza sheka zuwa jam’iyyar PDP.
Wata majiya mai tushe daga Karamar Hukumar Kankia sun tabbatar da cewa sama da wata uku Sanatan ya yi wata ganawar sirri da Shugaban jam’iyyar PDP a Karamar Hukumar Kankia.
Tun daga lokacin tattaunawarsu ke ci gaba a asirce.
Majiya a cikin jam’iyyar PDP sun ce Sanata Ahmad Babba Kaita ya gana da tsohon Gwamnan PDP, Alhaji Ibrahim Shema a Abuja.
An kuma yi wata ganawar a garin Kaduna su hudu, tsakanin Sanata Ahmad Babba Kaita, Alhaji Salisu Majigiri da kuma Ibrahim Shema da wani mutum daya.
Tattaunawar ta daddale amsar Ahmada Babba Kaita a jam’iyyar PDP da ba shi takarar Sanata daga yankin Daura ba tare da wata hamayya ba.
Majiyarmu ta tabbatar mana cewa, nan da ‘yan kwanaki kadan zai bayyana matsayarsa a jam’iyyar APC.
Ahmada Babba ya yi hira guda biyu wadanda ke nuna cewa akwai yiyuwar canza shekarsa.
Hirar farko da ya yi da sashen Hausa na rediyon Jamus, wadda suka dora a shafinsu na Facebook, inda yake cewa jam’iyyar APC ta sani in ta aikata kuskuren baya akwai wasu jam’iyyun.
Hirar ta biyu wadda ya yi da jaridar Daily Trust fitowar ranar 26/3/22, inda ya ce yana tattaunawa da mutanensa a kan makomar siyasarsa.
Rikicin APC a Karamar Hukumar Kankia ya sanya makomar Ahmad Babba Kaita a jam’iyyar ba ta da wani gurbi.
Ahmad Babba Kaita, shi ne Sanata mai wakiltar yankin Daura, ya yi Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kankia, Kusada da Ingawa har sau biyu.
Yana daga cikin Sanatoci masu aiki tukuru da aka samu a Katsina.
Yana kuma cikin ‘yan adawar da suka ba gwamnatin PDP wahala a Katsina.
Katsina City News
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar Taskar Labarai
@www.jaridartaskarlabarai.com
The Links News
@ www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245