SANATA MARAFA YA GOYI BAYAN HUKUNCIN KOTUN TARAYYA…ZASU KUMA DAUKAKA KARA….
Daga.Muhammad Ahmad …a Abuja
APC A Zamfara: Sanata Marafa Ya Goyi Bayan Hukuncin Kotun Tarayya, Zai Daukaka Qara Kan Hukuncin Kotun Jiha Ta Zamfara
Shugaban kwamitin albarkatun man fetur na Majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata Kabir Garba Marafa (Sanatan APC mai wakiltar Zamfara ta tsakiya) ya jinjinawa hukuncin da Babbar kotun tarayya, mai zama a Abuja ta yanke, inda kotun ta marawa INEC baya kan matakin da ta dauka na hana jam’iyyar APC yin takara a fadin Jihar Zamfara.
Idan dai ba a manta ba, a shekarar da ta gabata ne hukumar INEC ta yi watsi da sunayen ‘yan takarar da jam’iyyar APC bangaren gwamnati ta bayar, saboda rashin yin zaben fid da gwani ko cimma matsayar sulhu a tsakanin ‘yan takarar.
Marafa a takardar manema labarai da ya sake a jiya jim kadan bayan hukuncin da Mai Shari’a Ijeoma Ojukwu ta yanke, ya ce, hukuncin ya kawo qarshen qarfa-qarfa da kama karyar da gwamna Yari suke yi wa mutane a siyasar Zamfara, wanda hakan zai tilastawa Yari ritayar dole a siyasance.
Babbar kotun tarayyar ta ce, abin da hukumar INEC ta yi, ta yi daidai, domin ba hukumar ba ce ta hana jam’iyyar APC gabatar da zaben fid da gwani a Jihar. Ita wannan shari’ar ta Babban kotun tarayya da ke Abuja, wasu ‘ya’yan jam’iyyar APC ne suka shigar da ita, wadanda suka ce sun samu ne ta hanyar sulhu.
A daya bangaren kuma, Sanata Kabir Marafa ya yi shelar cewa, zai daukaka qara kan hukuncin babbar kotun Jiha ta Zamfara, wacce ke cewa, jam’iyyar APC ta gudanar da zaben fidda gwani a Zamfara, wanda APC bangaren Yari suka gabatar.