SANATAN FUNTUA :
..ZAN KARBI KUJERAR MANDIYA
………inji Muntari Dandutse
Kwanaki kalilan gabanin zaben fitar da gwanin jam’iyyar APC, dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Funtua da Dandume a majalisar wakilan Nijeriya Mukhtar Dandutse ya shirya tsaf domin ganin ya karbi kujerar Sanatan shiyyar Funtua daga hannun Bello Mandiya a zaben da APC zata fitar Dan takarar ta mai zuwa.
Mukhtar Dandutse na magana ne a babban gangamin da ya shirya a shiyyar Funtua somin bayyana aniyarsa ta neman tikitin takarar Sanatan shiyyar.
Dandutse ya yi nuni da cewa yana da gogewar da ta kamata da zai iya wakiltar shiyyar ta Funtua, inda ya lissafto wasu daga cikin nasarorin da ya samu a kasancewarsa shugaban karamar hukumar Funtua da kasancewar sa dan majalisar wakilai har karo uku a majalisar dokokin Nijeriya.
“Cikin wadannan shekarun, na samu damar gina makarantu, asibitoci da samar da ayyukan yi ga matasa da ba da tallafin sana’o’in hannu ga mata da matasa a yankin. Na yi alkawarin ci gaba da wadannan ayyukan muddin aka zabe ni a matsayin Sanata”, inji Dandutse.
Ya yi nuni da cewa yankunan shiyyar Funtua dake fama da matsalolin tsaro nan da can, na da bukatar jajirtaccen mutum mai gogewa da kwarewa domin shawo kan matsalar cikin kankanin lokaci.
Dan majalisar wakilan ya bukaci ‘ya’yan jam’iyyar APC da shugabannin ta da wakilai wato ‘delegates’ da su bashi goyon baya ya samu nasarar zaben domin shiyyar Funtua da daukacin jihar Katsina ta cigaba da cin moriya.
A nasa tsokaci, shugaban jam’iyyar APC na shiyyar Funtua, Ibrahim Danjuma Malumfashi, ya ce ba su day wani dan takarar da ya wuce Mukhtar Dandutse a kujerar Sanatan shiyyar.
Ya yi nuni da cewa Dandutse mutum ne mai gaskiya, juriya, hakuri da rikon amana da yake da son al’ummar sa a rai.
Shi ma da yake jawabi, jami’in hulda da jama’a na jam’iyyar APC a jihar Katsina Shamsu Sule ya yi takaicin cewa tun da Sanata Abu Ibrahim ya sauka daga mukamin Sanata a shiyyar Funtua, shiyyar ta rasa gatan da take samu. Ya ba da tabbacin cewa Mukhtar Dandutse zai dawo da martaba da kimar shiyyar Funtua tare da tabbatar da an tafi da kowa da kowa a cikin tafiyar.
Dubun dubatar jama’a dai ne suka hakarci taron gangamin da kwamitin yakin neman zaben Dandutse ya shirya.