Sarkin Kano Ya Ziyarci Wadanda Ambaliyar Ruwa Ya Shafa A Gwarzo
A yau ne Mai Martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi all, Ya ziyarci Karamar Hukumar Gwarzo domin jajantawa al’ummar garin da ambaliayar ruwa ya shafa wanda ya yi sanadin rushewar muhallan su tare da asarar dukiyoyin su, Sarki ya tallafawa wadanda iftila’in ya shafa.
Ka ji yadda ake adalin shugaba abin koyi mai tausayin talakawan sa, Sarkin ya samo wannan halin alherin nasa ne a irin tarbiyyar da iyaye da kakanni suka dora shi akan ta, ALLAH shi kara suttura da Arzuki da wadata da Daraja Darajar Sayyuduna Rasulillahi ( ﷺ ).
Daga: Masoyin Sarki Anas Saminu Ja’en