SHANU 700 ZA A YANKA A BA MABUKATA 4900 A KATSINA

0

LAYYA:
SHANU 700 ZA A YANKA A BA MABUKATA 4900 A KATSINA
@Muazu hassan
Wata Gidauniya wadda ke karkashin Da ga shiek Ibrahim inyas zata yanka shanu har dari bakwai a ranar sallah ta Raba ma mabukata da masu karamin karfi,a katsina.
Gidauniyar wadda ta dau shekaru Goma sha daya tana wannan aikin Alheri duk babbar sallar, a bana zata yanka shanu ga 2300 a jihohin katsina Kano da Kaduna.
A nan katsina har an kawo shanu dari bakwai wadanda za a yanka a ranar sallah. Kowane sa za a raba naman shi gida bakwai a raba ma mutane bakwai.
An tsara za a rabar da katin amsa ga gajiyayyu ,raunana da mabukata. Wadanda zasu taru a filin wasa na karakanda a raba ma duk Wanda ya samu katin.
A tsarin Gidauniyar ta na sayar da kai,kafafu,fata da kuma yan ciki na kowane sa akan dubu Goma da dari bakwai.
Wanda da kudin ake biyan wadanda sukayi hidima na aikin shanun tun daga yankawa,fida da rarraraba su.kashi kashi kamar yadda kowa zai dauka.
Wadannan shanun da za a yanka har sun iso katsina.inda gwamnan katsina ya bada inda za a ajiye su ana kula dasu har zuwa ranar sallah da za a yanka a rabar da naman sadaka ga mabukata.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
Www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245
Katsinaoffice@yahoo.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here