SHARHIN TASKAR LABARAI: GWAMNAN KATSINA; KO HAKA NE? Akan masu rike da mukamai ABUJA!

0

SHARHIN TASKAR LABARAI:
GWAMNAN KATSINA; KO HAKA NE? Akan masu rike da mukamai ABUJA!!

Daga Taskar Labarai

A jiya 22/12/2018 Asabar aka kaddamar da wasu gudummuwa ga matasa, wanda shugaban bankin bada bashi don gina gidaje, Arc Musa Dangiwa ya bayar ga wasu Yan jihar Katsina.

Kayan sun hada da na koyon sana’a da kuma na kamfen Wanda kudinsu ya kai miliyan ashirin da doriya. A wajen gwamnan Katsina ya yi wani zance, Inda yake cewa duk cikin wadanda akai baiwa mukami a Katsina mutum biyu ne kawai suka damu da yin wani na abu na samarwa matasan Katsina abin yi, wanda yake taimakon shugaba Buhari Katsina.

Ko maganar gwamna Haka ne? Ko tana bukatar karin haske? Da bayanai? Ko tana bukatar ai ma gwamnan matashiya.

Taskar labarai mun yi bincike daga jiya zuwa yau mun gano kamata yayi gwamnan na Katsina ya fayyace maganar sa dalla-dalla kafin ya fada, kuma kamata ya yi maganar tasa ya yi Mata sharhi da bayanai, ba kawai a dunkule da kudin goro ba.

Saboda da maganar shugaba kamar doka ce da umurni wasu ma suna daukar ta kamar wahayi ne. Don haka ake son kafin shugaba ya yi magana yayi zurfin bincike ya kuma sanya a kawo masa duk bayanan da yake bukata kuma in zai yi bayanin yayi shi a fayyace. na ajiye komai a muhallinsa.

Maganar gaskiya, wasu dake rike da mukamai a Abuja suna abin da suke, tsawon lokaci kuma masu tasari dai dai tsarinsu.Wasu suna da yadda suka tsara irin taimakon da suke bada wa .uma suna yi ba kuma a boye yake ba zamu zayyano wadansu da muka tabbatar.

1. Sanata Hadi Sirika tun da aka yi Katsina ba a taba minista dan Katsina da ya samarwa matasan Katsina aiki ba, kusan yanzu haka duk shiyya na ma’aikatar jiragen sama ‘yan Katsina da dama ke aiki a bangarorin.

Abin da Hadi Sirika yayi gwamnatin jiha kadai zata iyaja dashi.

2. Ahmad Rufa’i shugaban sashen tsaron kasa da kasa nadin shi bana siyasa bane, kuma aikinshi na sirri ne don haka, duk taimakon da ya kan bayar a sirrance yake badawa, yana taimakon sa ta hanyoyi da yawa ta hanyar mutane masu mutumci, kuma taimakon sa na tasiri sosai, idan gwamnan na son karin haske ya tuntubi mai shari’a Musa Danladi Abubakar ko Muhammadu Danjuma shugaban cibiyar Katsina Vocational Training Center ta MD Yusufu, za su yi masa karin haske.

See also  Bakatsine Ya Daukaka sunan Nijeriya a Idon Duniya

3.Hajiya Hadiza Bala Usman shugabar hukumar shiga da fice ta jiragen ruwa ita nata taimakon na daban ne mai tsari irin nasa na daban, domin ofis ta bude a jahar mai ma’aikata wadanda aikinsu shi/ne aiwatar da tallafin ga mutanen karkara/ga irin bukatunsu. Ayyukan sun shafi tallafawa makarantun Allo da zawiyoyi da makarantun Islamiyyu na karkara da makarantun Boko na karkara wadanda basu da abin zama ko kayan karatu da bada jari da kayan sana’a ga matasa, mata da maza daga cikin Inda suka amfana harda karamar hukumar Kafur da wasu mutane a Garin Masari.
Ayyukan Hajiya Hadiza Bala Usman suna da yawan gaske ta kuma Jima tana yi, wanda ayyukan suna nan an taskace su a hotuna maras motsi dakuma bidiyo.

Hajiya Hadiza ta kashe miliyoyi masu yawan gaske a wannan ayyukan nataa Katsina.

Wanda Taskar labarai ta gano bai damu da yin komai a Katsina ba, shi ne Farfasa Al’amin Muhammad shugaban sashen gina gidaje na kasa.( FHA) shi kuma tsohon shugaban kasa Jonathan ne ya bashi mukamin wannan gwamnatin ta kyale shi bata kore shi ba, shi babban aikin da ya yi shi ne sallamar wani dan Katsina mai babban mukami a hukumar ta (FHA) duk kuwa da wasu manyan Katsina da sanatoci sun saka baki, amma yayi kunnen uwar shegu da rokon su.

Don Haka mu a Taskar labarai muna rokon duk lokacin da shugaba zai yi magana yayi bincike kuma ya fayyace komai a jawabin sa.
Amma yin kudin goro, yana kawo rarraba da baraka bayyane a tsakanin manya. Hausawa kuma na cewa in giwaye na fada ciyawa ce zata sha wahala, wannan shi ne ra’ayin Jaridar Taskar labarai.
__________________________________________________________
Taskar labarai jarida ce dake da cikakkiyar rijista a bisa yanar gizo na www.taskarlabarai.com da kuma bisa shafukan sada zumunta na Facebook da Twitter da instigram da Youtube.

A ranar 12/1/219 zata bude shafin ta na turanci wanda ake aikin ginawa a yanzu a yanar gizo da sauran shafukan sada zumunta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here