SHAWARA GA MATASAN ‘YAN FIM: Kada Ku Dogara Da Ali Nuhu Da Adam Zango

0

Daga Ali Artwork

Ina kira matasan mu da suke sha’awar shigowa wannan masana’anta ta KANNYWOOD idan mutum zai shigo to ya nemi sana’a a cikinta kada ka dogara da daya daga cikin wadannan mutane (Ali Nuhu da Adam A. Zango) da tunanin cewar za su taimake ka tsakani da Allah, to ka yaudari kanka. Saboda dukkansu ‘yan jari hujja ne babu wanda zai taimake ka dan ka zama wani abu sai dan ka yi ta tashi a yaron su in kuma baku gamsu ba, to ku duba duk jaruman da suke taimaka wa ya taba zuwa ya fi su?

Daga sun ga ka fara tasowa za ka fi su to a nan ne za su yi ta maka mugunta har sai ka je kasa. Daga lokacin da ka kula da hakan ka yi kokarin daukar mataki sai ka ji sun fara maka gori suna cewa kai butulu ne.

Ina so jama’a ku dinga kula da hakan. Wannan rikice-rikicen da kuka ga yana faruwa shirya  shi suke duk karshen shekara, ba dan komai ba sai dan kawar da hankulan mutane a kan yaran da suke tasowa saboda suna gudun kar a daina yayinsu, dan haka bari su yi abunda za a yi ta maganar su a media.

Ni da kuke gani na mayar da hankali a kan wasan barkwanci tun daga lokacin da na kula ba za su taimaka min ba na koma na dogara ga Allah, wasu ma a cikinsu har dariya ake min ana ganin babu inda zan je, na ci gaba da hakuri a hakan a kwana a tashi abun ya fara shiga zukatan mutane har na samu aka turo mun da wani aiki daga Lagos. A lokacin nakira yaran daya daga cikinsu don su taya ni aiki amma sai ya hana su yi.

See also  "Idan na zama 'yar Majalisa Duk Namijin da aka kama yayi Fyaɗe sai an Dandaƙe shi." ---Aisha Balarabe Alaja Katsina ta tsakiya--

Daya kuma na taba neman alfarma ya yi mun tallah a lokacin ba ni da shafukan talla na nemi zan biya shi a kan ya min talla amma ya ki duk da irin wahalar da nake yi musu a lokacin. Sai gashi wata jaruma wadda ban taba yi wa komai ba magana ma ba sosai muke ba. Wannan jaruma ba kowa bace illa Hadiza Gabon ina yi mata magana kan kace me duk sai da tabi shafukanta na yanar gizo ta yi min talla, cikin ikon Allah sai gashi na samu alkhari sosai, kuma batare da ta karbi sisina ba.

Shi ya sa da JAMILA NAGUDU da HADIZA GABON ba zan taba mancewa da su ba. Na gode da alkairi da kuka yi min da kuma gudummawar da kuka bani a harkokina.

Don haka ina kiran matasan KANNYWOOD da ku kula da kyau kar a yi ta muku dadin baki da yaudara da sunan za a taimake ku har sai lokaci ya kure. Don haka ku tashi tsaye wallahi YOUNG GENERATION lokacin mune yanzu.

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here