SHEKARU 66 NA SHEKARAU
Daga Bello Muhammad Sharada
Yau Juma’a 5 ga watan Nuwamba 2021
Mallam Ibrahim Shekarau, Sardaunan Kano ya cika shekara 66 a duniya. An haifi Sanatan Kano Ta Tsakiya ranar 5/11/1955 a Unguwar Kurmawa ta Kano Municipal. Ya yi zaman rayuwarsa a Giginyu ta Nassarawa.
A tarihi Sardaunan Kano, malamin makaranta ne, firisifal ne, darakta ne, famanan sakatare ne, gwamna ne, dan takarar shugaban kasa ne, shugaban kungiyar duk wanda ya ke firinsifal ne, ministan Najeriya, Sanata a majalisar dattijai ta kasa.
Shekara 45 Shekarau ya yi yana yi wa Kano da Najeriya da Musulunci da jama’a hidima kuma Allah ya sanya wa wannan hidima albarka.
A aiki da mulki da siyasa da mu’amala da sarauta BAMBANCIN SHEKARAU DA SAURAN
Shi yana riko da amanar aiki gam-gam
Shi Yana karbar shawara daga kowa
Shi Yana baiwa kowa cikakken ‘yanci
Shi Yana bin ka’idar aiki da doka
Shekarau ba ya zagi da cin mutunci
Shekarau yana da tausayi da jinkai
Shekarau yana girmama dattijai da malamai
Yana da hakuri da juriya da yafiya
Yana jan Matasa da Mata a sha’aninsu
Yana da saukin kai da fahimta
A mulkinsa ya saka kowa ba kyama
A mulkinsa ya baiwa LG damarsu
A mulkinsa ya sallami ma’aikata da masu fansho da ‘yan siyasa
A mulkinsa ya saka saraki da ‘yan kasuwa
A mulkinsa ya sauke hakkin addini
A mulkinsa ya karfafawa talaka da marasa galihu
Sardaunan Kano yana shiga mutane
Sardaunan Kano yana zuwa jaje da ta’aziyya da dubiya
Sardaunan Kano yana limanci da Sallar gawa da hudubar rada suna
Sardaunan Kano yana hawa mumbarin siyasa
Shi ne gwamnan Kano kadai mai mata hudu
Shi ne gwamnan Kano kadai mai gida daya
Shi ne gwamnan Kano kadai malamin makaranta
Shi ne gwamnan Kano kadai malamin Alkur’ani da Hadisi da lissafi da Turanci
Shi ne gwamnan Kano kadai da wadanda suka samu sabani da shi a Siyasa basa tare da shi amma suka kame bakinsu a rediyo da jarida da New Media akansa.
Shi ne gwamnan Kano kadai da jam’iyyar hamayya ta zabe shi
Shi ne gwamnan Kano kadai mai kyauta da sadaka da sakin hannu
SHI NE SARDAUNAN KANO NA FARKO