SHEKARU HAMSIN DA HUDU (54) DA SHAHADAR SAYYID QUTUB IBAHIM:

0


NAZARI GAME DA LITTAFIN MU’ALIMUN FID-DARIQ
Daga Aliyu Ibrahim sani mainagge kano

A rana mai kama ta yau ne 29-08-1966 kimanin shekaru hamsin da hudu gwamnatin zalunci ta Jamal Abdun-Nasir ta zartar da hukuncin kisa ga fitacce kuma shahararren Malamin addinin musulunci kuma jagoora a kungiyar yan uwa musulmi Sayyid Qutub Ibrahim.
An haifi Sayyid Quxub Ibrahim a ranar 9 ga Oktoba 1906, a garin Musha ta qasar Misra, qwararren marubuci, malamin musulunci kuma jagora a qungiyar gwagwamayar musulunci ‘Ikhwanil Muslimun’. Marubucin shahararren tafsirin musuluncin nan ‘Fi-Zilalil Qur’an’ da kuma ‘Ma’alimun Fid-Dariq’ wanda sakamakon rubuta shi gwamnatin qasar Misra ta sa aka kashe shi ta hanyar rataya.
Kamar malamaisa Hasanal Bannah, shi ma ya tasirantu da fahimtar musulunci da qyamar turawan yamma wajen yaqi da aqidun musulunci.
A shkarun 1948 zuwa shekarar 1950 Sayyid Qudub ya halarci Jami’ar Colorado a Amurka, a nan ne ya rubuta littafinsa ‘Al-Adala al-Itijma’iyya fil-Islam’, wanda aka buga shi a shekarar 1949 a qasar Amurka. Haka kuma ya yi aiki a Jami’ar ta Colorado da kuma Jami’ar Stanford, haka kuma ya ziyarci mafi yawan manyan biranen qasar ta Amurka, ya karanci zamantakewar Amurka kamar yadda ya bayyana bayan dawowarsa a mukalarsa mai taken ‘Amurka Allati Ra’aitu’ Watau ‘Amurkar da na gani da ido na’. Bayan dawowarsa Misra a wajejen shekarar 1950 ya bar aikin gwamnati ya shiga qungiyar da Imam Hasan Al-Banna ya kafa ‘Ikhwanil Muslimun’ ya zama babban Editan jaridar Ikhwan, kuma babban xan majalisar shura na qungiyar. Tun daga lokacin ya yi ta karo da mahukunta qasar ta Misra qarqashin jagorancin Jamal Abdun-Nasir, bayan yunqurin kashe Jamal Abdun-Nasir da wasu masu kishin addini suka yi a shekarar 1954 ya jefa Quxub da wasu da yawa daga ‘yan qungiyar Ikhwan a kurkuku, inda ya shafe har tsawon shekaru uku a kurkuku. A lokacin zamansa a kurkuku ne Qutub ya rubuta fitattun littattafansa Tafsirin Al-Qur’ani ‘Fizilalil Qur’an (In the Shade of Qur’an)’ da kuma ‘Ma’alimun fid-Dariq (Milestone)’ wanda a cikinsa ya bayyana manufofi da qudurce-qudurcen musulunci da siyasa, ya kuma qalubalanci manufofin Turawan yamma. Littafin da gwamantin ta ce shi ne kundin manufofin juyin juya hali, da ta sanya ta haramta littafin, kuma bayan fitowarsa da wata takwas kacal, aka qara gurfanar da shi a gaban kotu, inda aka yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya, a ranar 29 ga Agusta 1966 kuma aka rataye shi.

GAME DA LITTAFIN MA’ALIMUN FID-DARIQ:
A shekarar 1964 ne kamfanin wallafa na ‘Kazi Publishing Company’ dake Egypt, ya buga shahararen littafin Ma’alimun Fix-Xariq, na Shahid Sayyid Qutub Ibrahim littafin da gwamnatin Misra qarqashin jagorancin Jamal Abdul-Nasir ta ce shi ne kundin juyin juya halin musulunci da ta ce yana barazana ga xorewar mulkin mahukunta qasar, wannan ce ta sanya aka gurfanar da marubucinsa a kotu, kuma aka yanke tare da zartar da hukuncin kisa ta hanyar rataya gare shi a ranar 29 ga Agusta, 1966.
Littafin Ma’alim Fix-Xariq ana sanya shi cikin fitattun litattafan da aka rubuta a qarni na ashirin (20 Centuary), saboda abin da ya qunsa na kyakkyawan tunanin musulunci, da hanyoyin gyaran al’ummah musulma wajen dawo da ita bisa tsarin shari’ar musulunci da Annabi (SAW) ya kafa a duniya baki xaya.
Littafin wanda ke xauke da babi-babi har guda goma sha biyu (12), an buga shi a shafi xari da sittin (160). A gabatarwar littafin, Sayyid Qutb ya buxe shi da nuni ga yadda jinsin xan Adam yake neman qarewa qarqaf, ba ta hanyar halaka ba, a’a ta hanyar canza tunanin xan Adam daga manufar halittarsa da Allah (SWT) ya yi zuwa bautar tunanin yammacin Turai, kamar yadda yake faxa cewa, “A yau duniya gaba xayanta tana rayuwa ne cikin jahiliyya ta gaske wadda duk ginshiqan rayuwa da tsaruka ke vuvvugowa daga gare ta, jahaliyya wadda duk kayayyakin jin daxi da qere-qere masu burgewa basu daxe ta da komai ba. Wannan jahiliyya ta xoru ne akan adawa da jagorancin Allah a bayan qasa, da kuma wata siffa mafi girma daga cikin siffofinsa, watau hukunci. A haka sai ta sanya sashensu zama iyayengiji ga sashe, kuma ba ta bayyana ta siffa sassauqa irin ta jahiliyyar farko da muka sani ba.
A babi na farko Shehin malamin ya yi bayani akan yadda qarnin farko ya kasance watau zamanin Manzon Allah (SAW) wanda ya canza al’ummar farko daga jahiliyya zuwa tsarkakakkiyar al’ummah, kamar yadda yake cewa, “Manzon Allah (SAW) ya yi nufin gina jama’a ce mai tsarkakakkiyar zuciya, hankali, ra’ayi da fahimta wadda gina ta ya tsarkake ta daga tasirin wani abu idan ba tsarin Ubangiji ba, wanda yake shi ne Al-Qur’ani.
A babi na bakwai (7) Shehin malamin ya nuna cewa ba wani tsari ne wayewa ba, idan ba musulunci ba inda yake cewa, “Al’ummar musulma ita ce al’ummah dake dabbaqa musulunci a aqida da ibada, a shari’a da tsari a halaye da xabi’a, sannan al’ummah jahila ita ce wadda ba ta xabbaqa musulunci, ba ta hukunci da shi a aqidance da fikirance, ba ta hukunci da qimominsa da tsarinsa da shari’o’insa da xabi’unsa da halayensa”. Ya ci gaba da cewa, “Al’ummah musulma ba ita ce wadda wasu gungun mutane ke kiran kansu musulma ba, alhali shari’ar musulunci ba ita ce dokokin al’ummar ba, ko da suna sallah, suna azumi suna hajjantar xakin Allah. Haka kuma al’ummah musulma ba ita ce wadda mutane ke qago irin na su musuluncin da wani abu koma bayan abin da Allah da Manzonsa suka tabbatar ba, sa’annan su ba shi sunan ci gababben musulunci.
A babi na qarshe da ya yi masa take da “Wannan ita ce hanyar”. Ya yi nuni da yadda xawagitai ke amfani da qarfi ta hanyar barazana ko xanxanawa masu kira zuwa ga musulunci azaba ta hanyar amfani da wuta kamar dai yadda aka yi wa As’habul Ukhdud, ko xauri, ko kora daga qasa, ko kuma kisa gaba xaya, amma dai tabbas nasara gare su take, haka nan halaka da tavewa ta tabbata ga azzalumai.
Akwai abubuwa masu yawa na tunanin musulunci da littafin ya qunsa da ba za mu iya kawo su anan ba, wannan ce ta sanya shekara xaya bayan buga littafin mahukuntan qasar ta Misra suka sa aka kama Sayyid Qutb tare da kashe shi ta hanyar rataye shi a shekarar 1966, wannan ce kuma ta sanya aka yi masa laqani da ‘Ash-Shahid’ watau wanda aka kashe a tafarkin Allah.
Haka kuma duk da yadda mahunta qasar suka haramta littafin an ce littafin ya zama mafi soyuwa a yankin larabawa da duniya baki xaya, inda aka ce an buga shi har kusan sau dubu biyu (2000), sannan an fassara shi da turanci da sunan ‘Milestone’. Mu ma anan Nijeriya an fassara littafin da Hausa da sunan ‘Alamomi akan hanyar da’awar musulunci’ wanda Sheikh Abubakar Mujahid shugaban qungiyar Jama’atu Tajdidil Islamy da Malam Ibrahim Musa Editan jaridar Al-Mizan suka yi a shekara ta 1415 AH.
Muna rokon Allah (SWT) ya yi jin qai ga Sayyid Qutb Ibrahim, ya karbe shi a matayin Shahidi, kamar yadda muke rokonsa ya sanya mu yi shahada a karshen rayuwarmu. Allah ya ba mu dacewa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here