Shugaba Buhari ya mika Ta’aziyya ga al’ummar Kano

0

Shugaba Buhari ya mika Ta’aziyya ga al’ummar Kano

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Shugaban ƙasar Nigeriya Muhammadu Buhari ya miƙa sakon ta’aziyyarsa ga iyalan fitaccen ɗan kasuwar nan ɗan jihar Kano Alhaji Shehu Rabi’u da gwamnati da kuma masarautar Kano bisa rasuwar ɗan kasuwar.

Hakan na cikin wata sanarwar mai ɗauke da sa hannun babban mataimaki na musamman ga shugaba Muhammadu Buhari, kan kafafen yaɗa labarai malam Graba Shehu.

Sanarwar ta cigaba da cewa, shugaba Buhari ya ce, rasuwar Alhaji Shehu Rabi’u babban rashi ne ga mutanen jihar Kano da ma Najeriya baki ɗaya, sannan ya bukaci al’umma da su yi wa marigayin addu’ar samun Rahamar Ubangiji.

See also  TURAKI YA YI FATAN KASANCEWA MAFITA GA AL'UMMAR NAJERIYA

Sanarwar ta ce, shugaban ƙasar ya kuma mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan marigayi shiek Isiyaka Rabi’u da kuma shugaban kamfanonin BUA Alhaji Abdulsamad Isiyaku Rabi’u.

Shehu Rabi’u dai yana daga cikin zuriyar Sheikh Isyaka Rabiu da ke Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here