Shugaban masu buƙata na kasa ya taya Musulmin Najeriya murnar zagayowar ranar Maulidi.

0

Dr, Hussaini Suleiman Kangiwa (“Sarkin Arawan Kabi”) Shugaban masu buƙata na kasa ya taya Musulmin Najeriya murnar zagayowar ranar Maulidi.

Daga: Comrade Musa Garba Augie.

Shugaban masu buƙata na kasa. Dr, Hussaini Suleiman Kangiwa ya taya al’ummar Musulmi murnar zagayowar ranar Maulidi a wata sanarwa da ya fitar.

Dr, Hussaini Suleiman Kangiwa ya ce ranar Maulidi rana ce da ya kamata Musulmi da sauran mabiya wasu addinan su tuna da alfanun zaman lafiya da girmama juna kamar yadda Annabi Muhammadu Salallahu Alaihi Wasallamya koya mana tsawon rayuwarsa ta tsoron Allah.

Ya ce yin hakan na da matukar amfani a yanzu da ake tsananin bukatar waɗannan halaye nasa don kawo waraka a ƙasarmu tare da karfafa danƙon zumunci a matsayinmu na mutane masu imani kuma ƴan Najeriya.

See also  An dakatar da Dagatai biyu da suka kwashe Tallafin Kurona a Kano

Ya kuma bukaci yan Najeriya su ci gaba da addu’a da tallafa wa hukumomin tsaro a koƙarinsu na kare yan kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here