SIYASAR MU A NAJERIYA

0

Daga Sulaiman Umar

A zaben 2019 in Saraki bai tsaya takarar Shugabancin kasar nan ba zai fuskanci fushi daga Ruhi mai Tsarki – Inji wani malamin addinin kirista
Wani babban malami kuma limamin addinin Kirista dake zaune a jihar Legas, Manzo Elijah Ayodele, ya roki shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki,akan ya nemi tsayawa takarar kujera ta shugaban kasa a zaben 2019.

Limamin ya yi gargadin cewa akwai mummunan sakamako ga Sarakin muddin ya ki neman takarar shugaban kasa a kakar zabe ta shekara mai gabatowa
Ayodele wanda shine babban limamin Cocin Inri Evangelical ya bayyana hakan a makon da ya gabata yayin sadaukar da wani dakin taro na zamani da yayi a unguwar Isheri-Olofin ta jihar Legas.

See also  JANAR BURTAI ZAI MAKA MAHADI KOTU

Ayodele yaci gaba da cewa,”Ubangiji ya na son ya yi amfani da Saraki wajen taka wata muhimmiyar rawa a kasar nan domin daidaiton wasu abubuwa da suka kauce daga turbar tsari.

Saboda haka Saraki ba shi da wani zabi face na tsayawa takara.”
Ya kara da cewa, “muddin ya yi rashin biyayya dangane da wannan lamari to ko shakka ba bu zai fuskanci fushi da azabar Ubangiji.”
(Hoto: Bukola saraki)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here