SOJA SUNYI MA YAN BINDIGA BARNA A NAHUTA BATSARI

0

SOJA SUNYI MA YAN BINDIGA BARNA A NAHUTA BATSARI
daga misbahu A batsari
Wani Hari da yan bindiga suka kai a daren jumma ar 20/8/2021 a sansanin soja dake garin Nahuta karamar hukumar batsari ta jahar katsina yayi ma yan bindigar mummunar barna.
Kamar yadda muka ji a cikin garin ranar alhamis da safe yan bindigar suka bugo ma mutanen garin Nahuta waya suka gargade su da cewa lallai kowa ya shiga gida a daren domin kuwa zasu kawo Hari.
Amma harin nasu ga jami an soja dake sansani a gari zaya tsaya.an tabbatar mana jama ar gari na samun labarin kowa yayi ta kansa tun farko yammacin ranar.
Wata majiya a cikin sojan tace da yake sojan sun samu labarin sai suka shirya masu.
Barayin da karfin hali sun shigo har cikin garin nahuta amma basu shiga gidan kowa ba, sai wasu shaguna biyu da suka fasa.sai kuma wani mutum da suka rutsa dashi a wajen suka bubbuge shi suka kwace masa kudi kamar yadda wani Dan garin ya tabbatar mana.
Bayan sun gama shawaginsu a cikin gari sai suka nufi sansanin na sojoji dake garin.
Dama sojan sun shirya masu.yan garin sunce rugugin bindigogi kawai kake ji.
Dole yan bindigar suka fara shiga daji kowa na ta kanshi.mutanen garin sunce sunji yan bindigar na ihu suna kiran yan uwansu da cewa ance a janye.
Da safiyar jumma a yan garin sun Kona gawar wani Dan bindigar da suka gudu suka bari.
Yan bindigar sukan dauki gawar nasu in an kashe don kar su barshi aga fuskarshi a gane ko waye.
In kuma zasu yar da gawar sukan Kona fuskarshi.yadda ko an ganshi kar a gane waye shi.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
Www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
Www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here