Sojoji sun kashe ‘yanbindiga uku sun kubutar da wasu a zamfara da katsina
shu’aibu Ibrahim daga Gusau
Rundunar sojojin operations Sahel sanity sun kashe ‘yanbindiga uku tare da kubutar da wasu wadanda akayi garkowa dasu tsakianin zamfara da jihar katsina.
Wannan bayanin ya fitone cikin wata takarda da aka rabata ga manema labaru, Wanda ke dauke da sa hannun ,
Birgediya Janar ABENARD ONYEUKO, Daraktan Ayyukan yada labaru na hukumar tsaro.
Darattan ya bayyana cewa wannan samamen, sojojin sun sami nasarar kawar da wasu ‘yan bindiga guda 3 tare da kwace bindiga kirar AK 47 guda daya, buhunan alburusai da AK 47 guda biyu da kuma kananan bindigogi 127 da kananan bindigogi 7.62mm.
Ya kara da cewa sakamakon bayanan sirri, sojoji sun kama wani da ake zargi da laifin fashi da makami mai suna Dahiru Liman a Ugwan Malama Rama. Binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin ya shiga hijira ne a cikin kauyen bayan rushe sansanoninsu da ke Bakin Lamba a yayin aikin kwantar da tarzomar da sojoji suka yi a yankin.
Ya ci gaba da cewa a wannan ranar dakarun da aka tura a Dandume LGA na jihar Katsina sun ceci wadanda suka sace 4 daga hannun wadanda ake zargi ‘yan fashi ne a kauyen Tudun Ali sakamakon bayanan sirri daga yankin.
A wani labarin kuma, a ranar 18 ga Agusta 2020, sojoji sun gudanar da bincike a wasu wuraren da ake zargin ‘yan fashi da makami ne, sun gano wasu bindigogi 5 da ke cikin gida a kauyen Unguwar Tsamiya a cikin garin Faskari LGA na Katsina, Wanda ana kyautata zaton maharan sun gudu daga inda suka buya, don haka suka bar makaman kafin dakarun su isa.
A ranar sha tara ga watan Agusta 2020, sakamakon bayanan sirri da suka ba da wanda ya bayyana yunkurin ‘yan fashi a yakin Marehe da Danlayi da
Bena tare da yiwuwar yin garkuwa da shanu a wani kauyen da ke kusa da Bena, sojoji suka hanzarta suka kuma yi kwanto a hanya tare da kama mutum 1 da ake zargi mesuna Bello Abdulrahman dauke da katari sai mutane 2 da suka tsere zuwa cikin daji. Wanda ake zargin a halin yanzu ana cikin binciken farko yayin da ake ci gaba da kokarin ganin an kama wadanda suka tsere.