SU WA KE MULKIN JIHAR KATSINA?

0

SU WA KE MULKIN JIHAR KATSINA?

Tare da Abdulrahman Aliyu

A kakar zaben 2015 al’ummar jihar Katsina suka fito tari guda domin su nuna shaukinsu na bukatauwar neman sauyi a yanayin yadda ake gudanar da jagorancin jihar daga jam’iyyar PDP da suka kira mai mulkin kama karya.

A lokacin akwai mutane da yawa da suka fito takarar neman zama gwamnan wannan jiha daga jam’iyyu mabambanta. Amma cikin ikon Allah aka zabi Rt. Hon Aminu Bello Masari a matsayin gwamna, duba da nagartarsa da kuma tunanin shimfida mulkin adalci da ake masa tunani.

An ta samun cece kuce daga mabanbantan mutane kan cewa Rt. Hon Aminu Bello Masari zai zama hoto ne kawai, wanda wasu da yawa suka sha karyata hakan na cewa duk wanda ya san shi ya san shi da jajircewa da kuma maida hankali wajen kawo cigaba ga al’umma.

Idan muka kalli jihar Katsina a yau zamu ga cewa kamar akwai wasu da ke mulkar jihar bayan gwamnan, ko kuma a ce jiya ce ta koma yau a jihar, ma’ana a bangaren ayyukan raya kasa ba mu gani a kasa ba.

Tun nadin kwamishinoni da gwamnan ya yi a zangon sa na farko alamu suka fara nuna akwai lauje cikin nadi a tafiyarsa. Misali yadda ya dauko wasu da suka baro jam’iyyar PDP ba da dadewa ba ya basu manyan kwamishinoni a jihar.

Ya dauko ‘ya’yan wasu ‘yan siyasa da suka nemi takara da shi ya basu kwamishinoni ba tare da la’akari da cancantarsu ba. Sauran mukamai ma da suka hada da SA da SSA duk ana ganin kamar gwamnan ya yi rabon ne kawai da bakin wasu.

A bangaren aiki kuwa gwamnan ya nada kwamitoci a bangaren Lafiya da ilimi tun tashin farko, inda suka yi aikin su suka kare, sai dai abun tambayar a nan shin bangaren lafiya da ilimi sun samu cigaba a jihar Katsina? Amsar ita ce basu samu ba.

A bangaren lafiya kowa ya san yadda gwamnatin ta tashi tsaye ta yi gyare-gyare a asibitocin cikin birni da kuma wasu zababbun asibitoci na wasu kananan hukumomin jihar. Amma aikin duk bula ne kawai domin a zahiri ba magani kuma ba ma’aikata, duk wanda ya zai fadi gaskiya kuma yake ziyartar wadannan asibitoci na gwamnati zai tabbatar da haka.

An yi wa gwamnan koken haka na sakaci da ganganci da ake da ayyukan gwamnati musamman a asibitoci, amma ya yi biris, duba da cewa wata kila masu juya akalar gwamnatin tasa suna da wani kaso da suke amfana da shi a bangare.

A bangaren ilimi kuwa nan ma ba wani cigaba da za a iya gwadawa wanda ya shafe na gwamnatocin baya da suka shude, misali gwamnan ya dena biyan kudin jarabawar SSCE ga dalibai, wanann ba laifi bane, amma wane tsari ya kawo wanda ya maye gurbin? Amsar babu.

Hakika ilimi yaga takansa a lokacin wannan gwamnati ta APC domin yanzu a jihar Katsina kaso 78% na dalibai kasa suke zama firamare da sakandire. Wani abu da ya ida fito da gazawar gwamnatin jihar Katsina shi ne a kaf din jihohin arewa jihar Katsina ce tafi yawan makarantun Al’umma. Wanda hakan ke nuna cewa jihar ta gaza a bangaren sanarvda wadattun makarantu, duk kuwa da cewa jihar ce ke mataki na shidda a duk kasar wajen ware kudi a bangaren ilimi.

Wani abun takaicimma shi ne yadda kudaden tallafimda ake ba daliban duk da basu taka kara suka karya ba, amma suka gagara shekara biyu da suka gabata.

A bangaren daukar aiki a fannin ilimin wannan jihar bata tantance wadanda take dauka, kawai wa ka sani ne wa ya sanka, yanzu abun ma ya kai a kafafen sadarwa ake ganin takardar shedar daukar aikin malaman makarantar. Akwai ma’aikatan Casual na ilimin da lafiya dake bin wannan gwamnatin kudin watanni biyar ta ki biya.

A bangaren hanyoyi da magudanan ruwa nan ana iya cewa Allah sam barka amma a cikin kwaryar garin Katsina kawai domin ba laifi an dan magance matsalar magudanan ruwa.

Amma duk hanyoyin da wannan gwamnati ta fara ya zuwa yanzu babu wanda ta kammala aikin duk tafiyar hawainiya ce, kawai, duk da cewa a kwanaki shugaban kasa ya zo ya bude wata hanya ta boge wadda ita ma ba a karasa ta ba, wadda ta tashi daga shinkafi zuwa Dankaba.

See also  Rashin Biyan Haƙƙoƙin Ma'aikata: Ya Durƙusar da Gidan Rediyo Najeriya

Wani abun takaici shi ne, yadda ake aikata banna amma gwamna bai kai idon sa wajen sai da kawai ya kawar da kai wata kila ko kunyar masu aikata bannar yake ji ko kuwa kawaici ne oho?.

Misali shekara guda da ta wuce gwamanu ya bada kudi domin a horas da ‘yan social media, amma abun ban haushi da takaici wani SSA ya yi kwance da wadannan kudaden ya yi gaban kansa da su. Akai ta fama amma abu yaci tura. Kamata ya yi ace gwamna ya biya masa kudin ya cire shi daga mukamin tun da bai da amana, amma sai ya yi biris da shi. Ya nuna kamar bai san ana yi ba.

Irin wadanann abubuwan akwai su da yawa a wanann gwamnatin amma an kawar da kai, dauki misalin irin yadda wasu kantomomi suka rika watsi da kudi da kuma juya ayyuka ta hanyar karakatar da kudi. Misali akwai shugaban karamar hukumar da ya gaje wani wuri ya maida shi matsugunnin jami’an tsaro. Amma ya rubuta sabon aiki ne ya yi, akwai kuma wanda aka ba kudin ‘yan gudun hijira ya yi sama da fadi dasu, akwai wanda aka sa ya gina asibiti a wani waje, ya sauya ta zuwa wani waje ya gayara wata da ke akwai a madadin sabuwar, akwai ma wanda tashin farko sauyawa ma’ajiyar kudin karamar hukumar wuri ya yi, sai da aka fatatake shi sanan ya dawo dasu. Amma a bangaren gwamna ba abun da ya yi masu sai dai ido kawai.

Wani abu da zai baka mamaki shi ne yadda gwamnatin ta ba kafafen yada labarai muhimmanci ta hanayar yi masu DG, SSA, SA, MA amma duk tarin wadannan mukamai da ya bada tarin kumfa ne a saman kogi, domin basu iya kare muradan gwamnatin, sai dai farfaganda kawai.

Basu iya fitowa su yi bayanin manufofin gwamnatin ga al’umma ko kuma wasu tsare-tsaren gwamnatin yadda mutane ba za su kosa ba sai dai kawai in gwamna yaje taro sui ta rige-rigen dora hotuna, wadanda kuma ba wannan ne cikakken aikin su ba.

Wani abun takaici shi ne yadda gwamnatin ke watsi da dukiyar jihar Katsina, musamman bayar da wasu kayayyaki haya ga wasu kamfuna, kuma kudin hayar ba wansa zai ce ma ga inda suke.

Watsi da wasu gine-gine da gwamnatocin baya suka yi, misali Dubai Maket, gidajen ‘Yan gudun hijira, Katsina shoping Mall da sauransu da dama. Ko shakka babu wannan ba cigaba bane, a ma iya kiransa da rashin sanin makamar aiki ko shugabanci, domin ko almubazaranci aka yi tun da dai dukiyar jiha ce kamata ya yi a san ya za a yi a inganta shi domin ya amfani jama’a.

Irin yadda wannan gwamnatin ta bi ta daddatsa duk wasu filaye dake jihar Katsina ba tare da la’akari da dacewar hakan ba shima kuskure ne da alamu ke gwada cewa akwai masu mulkin jihar Katsina bayan Rt. Hon Aminu Bello Masari, domin filayen duk ana raba su ne ga masu hannu da shuni da kuma ‘yan uwa da abokan arzuka.

Wani abun kuma da wannan gwamnati ta yi fatali da shi shi ne matasa, a gaskiya ya kamata ace matasa sun samu kaso fiye da wanda suka samu a wannan gwamnatin duba da irin gudumuwar da suka bayar.

Daga karshe ni ina hasashen cewa lallai akwai masu mulkar jihar Katsina daga bayan fage, wadanda suke kare muradansu na jari hujja, da kuma kokarin hana duk wani wanda suke ganin zai kawo wa jihar Katsina cigaba wanda bai biyo ta hannusa ba nakasu.

Muna fatan gwamnan jihar Katsina zai farka ya tuna da cewa shi ne al’umma suka zaba ba ‘yan jari huja ba. Kuma shi za a kira gwamna wanda ya yi nasara ko akasin haka ba wani ba.

Allah ya shige mana gaba

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here