SUNKAI HARI KAUYEN TSASKIYA TA JAHAR KATSINA
@ taskar labarai
Da asubahi (4:00am) ranar talata 27-10-2020 wasu mahara dauke da bindigogin bature suka Kai hari kauyen Tsaskiya dake cikin yankin karamar hukumar Safana ta jihar Katsina. Maharan wadanda ake zaton fulani ne masu satar shanu da garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa, sun samu tirjiya daga mutanen kauyen.
Mutanen sun jajurce akayi dauki ba dadi amma duk da haka ‘yan bindigar sun harbe wani mai tabin hankali wanda take ya mutu.
sannan sunyi garkuwa da wasu matan aure guda biyu, matan wani mahauci mazaunin kauyen.
Maharan sun saba zuwa kauyen ana fafatawa dasu, domin ko a kwanakin baya sunje kauyen amma mutane suka kora su.