TA ADDANCI A KATSINA:TSARO ADAWA DA KUMA AL’UMMA A HALIN DA AKE CIKI
Daga Danjuma Katsina
Cikin taimakon Allah, da amsar addu’a da jin tausayin sa, Allah ya fara kawo sauki a halin da jihar Katsina ke ciki.
Sauki na ce ba wai an bari ba, kasar ce baki daya ke cikin annobar tsaro ba Katsina kawai ba, amma tabbas daga abin da ke kasa. Allah mai amsar addu’ar wadanda cikin kunci, yana karba. Allah ya kara inganta tsaron a duk fadin jihar baki daya ameen.
A halin da ake ciki me ya kamata kowa yayi? Farko addu’ar da ake kar ayi wasa da ita, sannan duk duniya babu inda tsaro kacokam, yake hannun jami’an tsaro, kasashe mafi tsari da kudi a harkar tsaro suna dogara ga ‘yan kasa ne, wajen abubuwa biyu, bada bayanai da kuma daukar matakan gaggawa akan kansu.
Duk Wanda ya dogara da sai jami an tsaronmu sun cece shi cikin gaggawa tabbas kuwa in ba Allah ya kiyaye shi ba, sai ya zaman makoki ko jinya.
A kasar Saudi Arabiya, da Iran, Amurka, Rasha da Chaina da duk kasashen Turai, al’umma sune kashin bayan tsaronsu, sa ido da bada labari mai inganci. komai karfin kasa bata iya nasara ga tsaro in ba hadin kan al’umma don haka, ya zama wajibi jama’a su san ya zasu kare kansu da kansu ta sanya ido ga mugun da zai iya shigowa cikin su.
A kasashen da suka ci gaba ana koya ma mutane, su fada ma jami’an tsaro komai, in sun ga rayuwar su na cikin hatsari su kare kansu su dau mataki akan kansu, in bincike ya tabbatar da cewa a kare kai, ba abin da ake ma irin wadannan da suka samu kansu a irin wannan halin.
Amma barayin nan na daji,sun sa ma jama’a tsoron su, saboda suna tunanin basa iya komai sai jami’an tsaro sun zo,daya daga cikin barayin nan, da aka kama ya taba shaida mani cewa su hudu sun taba tada gari da itace, yace itace suka daga sama kamar bindiga aka yi ta gudu.
A kasashen da suke tasowa kungiyoyin sa kai masu tsari da horo suna taimaka wa a harkar tsaro, a nan matakin da gwamnati ta dauka na soke ‘yan sa kai kwata-kwata, kuskure ne da tsari ya kamata ayi masu, bisa horo da tarbiya da ingantawa, irin wadannan kungiyoyin hatta kasashen da suka cigaba suna amfani dasu. A inda basu bukatar tura jami’an tsaronsu na hakika.
Wani matsayi mai hatsarin gaske a tsaron jiharmu da jam’iyyun adawa suka dauka shi ne na ko in kula wasu ma na jin dadin abin dake faruwa dama ruruta shi, wasu ma har da daukar dawainiyar yada shi a manyan kafofin watsa labarai na duniya, don a nuna cewa jihar na lalacewa don basu ke mulki ba.ko kuma don an bata masu rai.
Wannan matsayin shi ne wasa da wuta mafi hatsari da jam’iyyun adawa ke yi. Tambaya a nan shi ne shin wai ‘yan ta’addar nan in sun zo suna bambamta dan jam’iyya mai mulki da Wanda ke adawa? Suna tambayar wake shiri da gwamnati wake baiyi?
Shin ba ‘yan Katsina abin ke shafa ba? Me ya sanya duk ‘yan jam’iyyun adawa basa yin komai sai bada labari kawai da yada shi? Tun da Katsina ke cikin halin da take ciki! Tsohon gwamnan jihar ta Alhaji Ibrahim Shema ya taba jajantawa? Ko ko dan takarar gwamna a jamiyyar PDP a zaben 2019 Alhaji Yakubu Lado Danmarke ya taba kai ziyarar jaje?
Wannan misalin ne kawai, akwai jam’iyyun adawa masu yawa a Katsina, me sukayi ?
Babu abin da suka kware, sai yada labaran da sharhi, amma babu neman mafita, ko kawo dauki don a samu mafita, wasu ko jaje ma basu taba yi ba.
Yanzu idan bisa tsarin Allah, sai wata daga cikin su ta amshi mulki, sai suyi tsammanin samun goyon baya daga wadanda suka kayar?
A kasashen da suka ci gaba, da wadanda suka san me suke, maganar tsaro ta lafiyar Al’umma babu ruwanta da adawa shi yasa ake cewa, basa canza gwamnati in kasar na a cikin barazanar yaki, sai lamarin ya wuce suke, tace rawar da kowane shugaba ya taka su ladabtar dashi.
Ya kamata jama’ar katsina su sa ido suga wace rawa jam’iyyun adawa ke takawa? A halin da tsaron jahar mu ke ciki?
Wasu kuma yan jam’iyya mai mulki ne, amma an bata masu rai, kila rigimar cikin gida kila ba kwangilamusamman yanzu da tattalin arzikin kasashen duniya ya shiga masassara ba kwangila ba mukami ba kudin da za a basu na kashe wuta.
Don haka, sai suga ruruta maganar tsaro da fatan tabarbarewar shi ne makaminsu, wannan shima wani ganganci ne mafi hatsari.
Daga cikin aikin jama’a zasu yi ma kansu wace rawa kowa ke takawa? Wani zai bada labari don ya jawo hankalin gwamnati wani don batanci, wani don ya yada fitinar kowa ka tantance kayi masa adalci ga aikinshi.
In muna son nasarar da Allah ya kawo ,mana ta fara samun sauki ta dore, dole sai anyi aiki kafada da kafada.kuma kowa sai ya shigo a ciki