Tabbas ina nan a kan bakata ta na sayan kungiyar Arsenal – Dangote

0

Tabbas ina nan a kan bakata ta na sayan kungiyar Arsenal – Dangote

Daga Zubairu Muhammad

Attajirin dan kasuwa da yafi kowane bakar fata kudi a nahiyar Afrika.

,Alhaji Aliko Dangote ya jadada cewa har yanzu yana kan bakarsa na son
sayar kungiyar kwallon kafa ta Arsenal dake birnin Ingila.
Dangote yace da zarar ya kammala aikin matatan man fetur da
yake ginawa a kan kudi $10 biliyan, zai mayar da hankalinsa kan
batun sayan kungiyar ta Arsenal.
“Idan na kammala matatan man, zata rika samar da gangan mai
650,000 a kowace rana kuma hakan ya nuna cewa zata zama
matatan mai mafi girma a nahiyar Afirka.
Tabbas ina nan a kan bakata ta sayan Arsenal ”
Dangote ya yi wannan maganar ne yayin wata hira da ya yi da
Financial Times da aka wallafa a ranar Laraba 11 ga watan Yulin.
A kididigan adadin arzikin da attajiran duniya suka mallaka da
Bloomberg ta wallafa cewa Damgote ya mallaki $12.4 biliyan,
wannan na nuna ya dara wanda yafi kowa hannun jari a kungiyar
Arsenal, Stan Kroenke, da $4.4 biliyan.
” Idan na sayi kungiyar, zan inganta ta yadda masu goyon bayan
kungiyar ke bukatar suka ta kasance”
Wannan dai ba shine karo na farko da Dangote ya nuna sha’awar
sayar kungiyar ta Arsenal ba.
A watan Satumban 2016, ya shaidawa gidan talabijin na
Bloomberg cewa “Babu makawa” zai saya Arsenal “matsalar ba ta
kudi bane

See also  Katsina United sun bamu Kunya...yakamata a sauke Shugabannin su. -Umar Isyaku Ogunse

“Wata kila cikin shekaru uku zuwa hudu,” inji shi.
“Matsalar shine akwai wasu ababen da suka shige min gaba. Da
zarar na kawar dasu, zan mayar da hankali kan batun cinikin. “

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here