TABBATAR DA SULHU A KATSINA : TAFIYA MAFI HATSARI DON GANIN KWAKWAF

0

TABBATAR DA SULHU A KATSINA : TAFIYA MAFI HATSARI DON GANIN KWAKWAF

Daga Taskar Labarai

Zuwan da gwamnan Katsina yayi a Batsari da Jibia ya ba jaridar nan damar samun wata alaka ta jarida da wasu fulanin dake a cikin daji, wani da muka lura yana daukar bidiyon abin dake faruwa a tsanake kuma yana aiki kamar wani dan jaridar su, ko kuma dan leken asiri muka nemi karin kusancin dangataka dashi, don rika tuntubarsa gaskiyar lamari koda ya faru.

Ya amince ya karbi lambobin wayoyinmu amma yaki bamu tasa yace su basu da tsayayyar lamba, bayan sulhu ya rika bugowa akai, yace yana gaisuwa ne da sada zumunta, wata rana sai muka ce masa me zai iya bamu tabbaci da shi cewa sulhun da aka yi yana tafiya? Sai yace muyi tunani, bayan shawara muka tsara cewa zai iya bi damu hanyar Danmusa zuwa bBatsari lami lafiya?

Yace mu shirya, mun dau kwanaki shidda muna addu’a da istihara, muka tsara matakin da zamu dauka koda wasan ya baci.

A ranar jumma a 13 ga satumba 2019 wakiliinmu ya kasance a gaban sakatariyar karamar hukumar Danmusa, kamar yadda aka tsara da karfe tara na safe.

Tara da minti Goma sai ga Alu ya bayyana da babur irin bajaj din nan sabo aka dan yi rana yace, “muna iya tafiya” nace Bismillah.

Tafiya ce ta kilomita sittin da biyar kamar yadda na kirga kuma zamu ratsa hanyoyi da yanki masu hatsari da an bar binsu saboda Fulanin sun kwace su.

A hanya ya fada mana cewa shi baya cikin masu dauke da makamai, amma shi aikinshi shiga gari ya sawo abinci, katin waya da shako labari, yana kuma shiga yanar gizo yaji me ake fada ya gaya ma ogoginsa.

Daga Danmusa mun ratsa garuruwa kamar haka kamar yadda na tambaya ana fada mani ina rubutawa, garuruwan sune; Marar Zamfarawa, Marar Katsinawa, Dandiri, Guzurawa, Dankula gGobirawa, sai Runka, sai mMarina, Garin Gambari, Bakurawa, ‘Yan ukku, Kirtawa, Kuka, Sabon garin ‘yar Gamji, Wagini, Garin Kobani, Kurna, Baka sSabo sai Batsari.

Mun iso Batsari a ranar ana wani taro da shugabannin Fulanin na daji a sakatariyar karamar hukumar Wanda Alu yace zai halarta ni kuma in wuce Katsina ko’in tsaya inga wainar da za a toya.

Hanyar da muka biyo ita ce hanya mafi hatsari a jahar Katsina, kuma naga tabbas muna labari a tsanake abin da rika gani ya sanya wuta dauke mani ban sake cewa kanzil ba sai da na ganni cikin tsakiyar Batsari, ban kuma dawo hayyacina ba sai da na ganni a gadon matata.

See also  Gamayyar Kungiyoyi A Katsina Masu Suna (Coalition Of Katsina Group For National Unity & Integration) Sun Kalubalanci Atiku Abubakar 

Tabbas hanyar bata biyiyuwa kodan sulhun sai dan ina tare da dan gidansu.
Muna tafiya tsakanin Kirtawa da ‘Yan uku wasu kawai suka tare mana hanya sai naga yayi, masu wata alama sai suka janye sai ya tsaya suka dade suna Fulatanci sannan muka wuce. A Guzurawa wani yaro karami ya tsaya tsakiyar hanya, muna tsayawa wasu suka fito daga cikin daji sai yayi wani kirari da Fulatanci sai suka iso aka rika tabawa ana jinjina. A Marina wasu Matasa na gani da kakin soja suna kwallo a gefen hanya suka tsaida mu yana tsayawa yayi masu wani zaurance sai suka fara ihu. A tafiyar sau shidda ana tsaida mu, sau uku muna tsayawa don Kan mu tsayawa tara ke nan.

Ba inda naga kowa da bindiga amma ga alama makamansu na nan kusa za a iya dauko su cikin mintoci in ta kama kuma ga alama hanyar suna sanar da na gaba abin da ke tafe,kila in ka tsira ga na farko na biyu zasu shirya maka .

Na gani matansu da yaransu suna rayuwa a dajin hankalin su kwance kuma a tsanake amma da sun ga bakon fuska sai hankalin su ya koma kanshi ga filin noma mai kyau fayau ba a noma ba.

Abin da ya daga mani hankali naji lokacin da wani ke masa wasa a kusa da Marina cewa, yo ka wuce dashi mana kawai wannan ai tsuntsu ne daga sama gasashshe, sai yace a a Alkawalin ba haka yace ba.

A Batsari na tsaya na halarci taron da aka yi wanda kantomomin kananan hukumomin Batsari da Jibia suka jagoranta, wanda wakilan Fulanin dajin kusan dari suka halarta sannan na wuce gida.

NB

Taskar labarai na da tsarin sakaya sunan marubucin da ya yi wani rubutu don dalilan tsaro da tsarin jaridar na cikin gida wani rubutun kuma suna kawo suna.
……………………………………………………………………….
Taskar labarai jarida ce da ke bisa yanar gizo a shafin www.taskarlabarai.com da kuma sauran shafukan sada zumunta. Tana da ‘yar uwarta ta Turanci mai suna The Links News dake shafin www.thelinksnews.com lambar waya ko whatsapp 07043777779.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here