TAKARAR YAKUBU LADO A PDP KO WASAN KWAIKWAYO?

0

TAKARAR YAKUBU LADO A PDP KO WASAN KWAIKWAYO? ~~~~ASIRI YA TONU

Daga Taskar labarai

Kwanakin nan wasu ‘yan jam’iyyar PDP na ta fasa kwai a kan takarar gwamnan Katsina a jam ‘iyyar a zaben da ya gabata.

Bayan kammala zaben, bayanai na ta fitowa wanda ya sanya Taskar labarai ta yi bincike na musamman, a binciken mu mun tattauna da wasu da abin ya shafa mun ga wasu takardu mun kuma ga wasu sakonni wayar hannu da aka yi musaya tsakanin wasu jigon PDP, abin da mu kaji daga gani ya bamu mamaki, da har muka fara tambayar anya takarar Lado a PDP ba wasan kwaikwayo bane aka yi?

Bincike da mukayi ya gano yadda Shema a matsayin sa na uban PDP a jiha ya rika zawarcin wasu yan APC akida don su shigo PDP ya basu takarar gwamna, abin da ya kira wadanda ke a cikin jam’iyyar, babu wani da ya cancanta ya yi takarar.

Daga baya Shema ya canza, shawara akan abin da wasu suka yi zargin cewa Shema baya son ganin wani mai ilmi da wayo ya samu daukaka fiye da shi.

Taskar labarai, taga wani wani sakon waya da wani ya tura ma sakataren PDP na kasa sanata Tsauri, a ciki yake cewa, “….da ku/ka nemi in dawo PDP abin da kuka fada mani daban yanzu kuma kun yaudare ni”.

Dare daya Shema ya canza shawarar kuma ya fara aikin ya za’ ayi Yakubu Lado ya zama Dan takarar PDP.

Bayan da lado ya zama Dan takara ta hanyoyin da aka sabawa ka’idar da aka cimmawa a zaman da ‘yan takara suka yi a Kaduna da Katsina, kamar yadda yan takarar su ka yi zargi.

An kafa kwamitin yakin neman zabe, amma na hoto na jeka nayi ka. Kamar yadda yan kwamitin suka tabbatar wa Taskar labarai.

“Duk wata shawara da muka bayar ba a dauka, ba a taba kiran taro ba na ya za a ci zaben mutane hudu kan zauna su yanke shawara su aiwatar, mutanen hudun sune, Ibrahim Shema da Salisu Majigiri da Yakubu Lado da Ibrahim Dankaba”. In ji wani jigo a tafiyar ta PDP.

An nuna wa Taskar labarai wasu takardun da suka shafi yakin neman zaben wanda kwamitin yakin neman zaben ya tsara.

“Ka gan su duk a banza babu wanda aka yi amfani da su haka mu ka yi rubutun banza, ba wanda ya san nawa dan takara ke kashewa a kudinsa, ba wanda ya san nawa ya amso a matsayin gudummuwa”. Inji wani jigo a tafiyar ta PDP

See also  WANI DAN SIYASA DA YACI ZABE.

DA KUDIN WA AKAYI ZABE?

Wani jigo yace, “kudin da aka/yi zabe da su na farko dana biyu, kudin da Atiku ya bayar ne, PDP a Katsina ta samu naira bilyan biyu daga wajen Atiku a zaben shugaban kasa aka kashe naira miliyan dari takwas kamar yadda lissafin yake, (an nunawa Raskar labarai jadawalin yadda aka kashe kudin).

A zabe na biyu kuma miliyan dari shidda aka kashe, suma kaga jadawalinsu ya kama naira bilyan daya da dubu dari hudu”.

Sauran miliyan dari shidda fa? Zarge-zarge ke yawo a kan su kamar yadda Taskar labarai ta tabbatar.

“Wasu gudummuwar da ake zargin ko dan takara da jam’iyya sun samo ba wanda ke da tabbacin su, an samo oho, ya akayi, dasu oho? In ma har an samo?” Inji wani jigo a PDP.

DAN TAKARA YA BADA KUDINSA?

Bincikenmu yace, in ma ya bada, kila sai dai dubu biyar da ya rika badawa asibiti, amma ‘yan kwamitin kamfen sun ce basu gani ba. “Naira miliyan daya da rabi ‘yan social media na jam’iya da na kamfen suka nema a basu su kafa ofishin amsar bayanan gaggawa lokacin zaben basu samu ba. Miliyan daya da rabi aka nema na kiran taron kungiyoyi masu goyon bayan PDP ba a samu ba” inji wani jigo a yakin neman zaben.

“Ana gobe zaben gwamna ba a rabar da kudin aiki ba sai goma na dare, kuma kudin duk suka zo da gibi, wani abin da zai baka mamaki, sam duk da muna kishin ai nasara muna aiki tukuru, in muna tattauna matsalolin dake gabanmu, shi in ka kalle shi sam ko a jikinsa, ba wata damuwa ko fargabar komai, kamar wanda dama ya san, ina ya dogara?” Inji wani jigo.

ME KUKA SANYA GABA YANZU?

Duk wadanda jaridar ta yi magana da su, sun ce ‘yanto jam’iyyar yanzu shi ne a gabansu? Kwato ta daga hannun su Ibrahim Shema da waziransa, da maido ta wajen talakawan Katsina shi ne ke a gabansu.

“In jam iyyar ta samu yanci..zaka ga me zai faru gaba” inji mai maganar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here