Talakawan Jahar Kano Abinci Sukeso Basu Buƙatar Talabijin
Daga: Murjanatu G Hassan (Murjanatu Diri)
Ina kiraga gwamnatin jahar kano Dr, Abdullahi Umar Ganduje kudin dazaka yi amfani dasu wajen siyan Talabijan da talakawa ka siyoma abinci ka raba musu domin rage raɗaɗin dayake damunsu.
Kokuma kabasu jari domin dogaro dakai hakan zaifi musu amfani a halinda ake ciki na tsadar rayuwa sannan zasufi ganin mutuncin gwamnatinka akan talabijin dinda zaka raba.
Tambayata anan shine ana kallon vedio ba’aci abinci ba?