Taliban: Shari’a, Jahilci da Rashin adalcin Musulmi

0

Taliban: Shari’a, Jahilci da Rashin adalcin Musulmi

Daga Fatuhu Mustapha

Kusan shekaru 16 da suka wuce na taba yin wani rubutu a zauren majalisar Finafinan Hausa, wanda na kira da Misrepresentation of Sharia in Hausa Film: The case of Maraba da Shari’a. Ina ganin in har da mutanen da a duniya basu fahimci me Allah yake nufi da saukar da sharia, to musulmi ne. A kiyasi na, sama da kashi 90 cikin dari na musulmi sun wa sharia wata mummunar fahimtar. Akasari abinda yake fara zuwa zuciyar mutane shi ne, yanke hannu, rajamu, zubar da jini da bulala. Kadan ne suke tunanin Zakka, zumunci, hana satar kudaden gwamnati, hana cin hanci da rashawa, samar da ruwan sha, samar da ilmi mai inganci ga kowa da kowa, rage yaduwar cututtuka irin su HIV, saboda tsoron Allah ya gamu da wadata an daina zinace zinace, wadata ta sanya an daina bara. Masu Sanaa suna biyar haraji, gwamnati kuma na amfani da harajin don cigaban talaka da sauran su.

A wani taro da Center for Contemporary Studies ta shirya akan sharia a Abuja a 2006. Farfesa Jibril Aminu ya yi wata magana da ta sani a cikin zuzzurfan tunani. Inda ya ce “ba za a auna nasarar da sharia ta samu da yawan mutanen da ta yankewa hannu ba, ko yawan mazinatan da ta jefe ba. Za a auna nasarar sharia ne, da raguwar masu kamuwa da cutar HIV saboda Allah ya hana zina, za a kirga ta ne da yawan ingantattun makarantun da sharia ta samar, saboda ilmi wajibi ne a musulunci, yawan bishiyoyin da ta shuka saboda muhimmancin samar da bishiyoyi a musulunci. Su ma su Dr Bala Muhammed da Alkasum Abba a wata kasidar su, sun bayyana cewa, matukar sharia za ta yi wani tasiri a al’ummar Arewa, to sai ta kalli irin kalubalen da yake gaban al’umma ta magance su, kamar samar da ruwa mai tsarki, tunda ba a ibada sai da tsarki, ba kuma a tsarki sai da ruwa mai tsarki. Dole kuma sharia ta yaki jahilci domin jahilci bai da gurbi a addinin Musulunci, ya kuma zama wajibi ta samar da ayyukan yi, domin hadisai sun nuna illar zaman kashe wando. Matukar sharia ba za ta yi wannan ba, to kuwa ba ta da wata rana acikin al’umma. A wannan dalilin ne ya sanya nake jinjinawa gwamnatocin musulunci dake Saudiya da Iran saboda ina ganin wayannan su ya kamata su zamarwa duk wani mai rajin kafa sharia abin kwaikwayo. Duk kuwa da gazawar gwamnatin Saudiya wurin baiwa sauran musulmi yancin bin fahimtar su ta addini. Amma dai sun nuna irin yadda gwamnatin Shari’a ya kamata ta zama.

See also  Yadda Kasar European Da Norway Suke Shuka Dankalin Turawa Hade Da Kifi Waje Daya

A yau a kasar nan, abinda jihohin da ke tinkaho da kafa sharia ke iya nunawa na cigaban da sharia ta kawo bai wuce sabuwar hukumar Sharia Commission ba da Hisba Board. Wanda dukkan su ba wani abin ku zo ku gani da zaka nuna da suka kawowa al’umma. Banga wata hujja ta kafa Sharia Commission a jihar da kashi 99 na alummarta musulmi bane. Su kuwa hisba in ma tana da wani tasiri bai wuce na fasa kwalaben giya ba. Dukkan sauran hakkokin da aka daura mata, kamar yadda Shehu Abdullahi Fodi ya kawo a littafin sa, Dhiya Ul lil Ihtisab an wancakali da su.

Wani babban fagen da masu rajin kawao sharia suka gaza shi ne batun yancin zamantakewa, kawance, zabi, da na rayuwa. A yanzu haka a kasar Afghanistan da kasashen dake karkashin ISWAP ba ka da wani yanci, illa kabi dokar da suka kafa maka. Baka da damar ka yi magana, yanzu hukumci zai hau kanka. A kwai lokacin da yan Al AQIM suka kafa dokar hana sa ring tone q waya, in kuma aka kama ka, to hukunci zai hau kan ka. Irin wadannan hukunce ne za su biyo bayan nasarar taliban a Afghanistan. Ba ruwan su karbar zakka, ba ruwan su da samar da ruwan sha, ko inganta harkar noma. Su dai bukatar su a kawo mai laifi su yi masa hukunci. A iya sanina wannan ba ita ce sharia da manzon Allah SAW ya zo da ita ba. Domin kuwa ayoyin haddi a qur’ani kacokan basu kai 11 ba, amma ayoyin zakka, ilmi, ciyar wa, zaman lafiya sun fi misali a littafi Allah.

Ni dai har yau na kasa gane, wai wannan sharia da su Ahmqd Sani suka kawo mana, da wacce yan BH ke kokarin sai sun kakaba mana, da waccan ta yan taliban, inda aka samo su. Domin dai na yi imanin ba ita ce wacce manzon Allah ya zo da ita ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here