Tarihin Alhaji Haruna Kundila 1832 – 1902
Daga Fatuhu Mustapha
Ina ganin kan masu karatu zai kulle in suka ji irin zurfin tunani da Allah ya baiwa wannan mutum. Wani nazari da aka gabatar a Jami’ar Cambridge akan salon kasuwanci na Kundila, ya tabbatar da cewa, tunanin wannan attajiri ya girmi lokacin sa. Nazarin ya yi nuni da cewa, ko a wannan zamani tattalin arzikin duniya zai koyi darussa daga irin salon kasuwanci na Kundila. Kafin mu je ko ina dai, Kundila ba wata ja cikakken dan jari hujja ne, da ko Adam Smith da su Rostchild dole su duka masa.
An haifi Haruna Kundila a shekarar 1832, a unguwar Lolloki da ke cikin Birnin Kano. Sunan mahaifin sa Amadu, sunan mahaifiyar sa Aisha. Ya fito ne daga kabilar Kutumbawa, ana zaton yana da alaka da Ciroman Kano Danmama, kila ma jikan sa. Ya fara karatun sa a makarantar malam Sidi tun yana yaro karami. Da ya fara girma sai ya shiga sana’ar garuwa tun yana dan shekara 12. Da wannan sana’a ya fara tara jarin sa, har sai da ya kai shekara 24, daga nan sai ya fara sana’ar sayar da kaya. Da ya shekara 30 sai ya fara tafiya fatauci zuwa Kasashen Gwanja yana cinikin goro, ya na kuma sayen bayi ya kai Adamawa da Azben da Kamaru da Bauchi da sauran su. Da ya kara karfi sai ya fara kafa masana’antar yin kadi (yin zare), ya kuma kafa marina tasa ta kan sa. Kundila bai tsaya anan ba, ya kafa shaguna a Kwari inda duk abinda aka sarrafa a masana’antun sa, to shi da kan sa zai sayar a Kasuwa, wato dai ya kashe yan tsakiya (middle men).
Da ya karfi sai ya shiga harkar bayar da bashi (credit and loan). To amma saboda sanin hatsarin da yake cikin sana’ar sai ya shiga siyasar Kano, domin ya samu shiga wurin hukuma a bashi damar kafa dokokin da za su tsare masa dukiyar sa daga masu cinye bashin da suka karba.
Ya yi wannan dabara ne, a lokacin da aka nada Sarkin Kano Bello (1882 -1893). A lokacin da za a tafi Sakkwato domin yi mubayi’a kamar yadda yake a al’ada. Kundila ya lura da Bello talakan dan Sarki ne, saboda ya fi maida himma a malanta. Don haka sai ya bayar da keso guda a matsayin gaisuwa ga Sarki, wato wuri ko farin kudi 1000 kenan. Da Bello ya tambaya aro ne ko kyauta, sai Kundila ya ce “Allah ya taimaki sarki ina ni ina baiwa Sarki bashi?” Da Bello ya dawo sai ya samu aka kira masa shi, ya ce masa ya fadi duk abinda ya ke so, zai masa. Sai ya ce wa Sarki, shi baya bukatar komai. Abinda ya ke so kawai shi ne, Sarki ya yi dokar duk wani dan Kasuwa da aka kama a Kasuwar Kurmi da laifi, indai a wurin sa ya zo sayayya to a sake shi. Sarki kuwa ya amince masa. A saboda wannan doka ya kwacewa da yawa daga yan Kasuwa kwastomomi. Kusan kowa ya taho Kasuwa wurin Kundila zai je sayayya.
Kundila ne ya fara kirkiro da sabbin hanyoyin kasuwanci na saye da sayarwa a Kasuwar Kurmi. Shi ya kirkiro da tsarin kasuwancin nan ta hanyar lamuni, ka saya ka biya nan gaba, amma fa in farashi ya tashi sai ka yi ciko. Shi ne ya fara tsarin bashin nan na “A mirgina” wato (rollover), tun a lokacin Kundila yana karbar collateral in zai bayar da bashi. Sannan ya kawo tsarin bashi ta hanyar jinginar. Ka bayar da kadarar ka a baka bashi. Shi ne ya kirkiri tsarin yan sa ido, wato Loan Security, in an baka bashi, to akwai bayin sa da suke sa ido a kan ka, don kar ka gudu ko ka samu Kudi ka ki biya. Bayin sa na list na dukkan wadanda yake bi bashi, kuma kowanne rukuni na masu daukar bashi akwai irin bayin da ke kula da su.
Hausawa kan ce “ba na sayarwa bane, ya gagari Kundila” abinda ya sanya haka, saboda shi dai bai yadda akwai wani abu da ba shi da market value ba. Ance ya taba bayar da bashi da jinginar kashin awaki. Mutane suna ta mamaki, amma shi yana nufin takin da zai samu daga kashin awakin. To amma kuma ai duk kudin da yake da shi, in abu ba na sayarwa bane, ai ya gagare shi. Wato dai ana nufin komai zai iya saye, sai dai in ba na sayarwa bane.
Allah ya yi masa rasuwa a 1902 shekara daya kafin turawa su ci Kano.
Allah ya jikan sa ya yafe kurakuransa.