@ katsina city news
Aminu waziri Ya yi karatu Galadima Firamare dake Malumfashi a shekarar 1979 – 1985, Sannan ya je Secondary School Musawa inda ya kammala a shekarar 1991 ya kuma shiga Kaduna Poly 1992-1997 ya yi jami’ar Bayero 2008-2010, jami’ar Noun 2016-2017 jami’ar Sains Malaysia 2012-2013 da 2013-2016 da kuma jami’ar Sussex dake UK 2020 zuwa yau.
Wannan ya ba shi damar mallakar Digirin Digirgir kan kan Kimiyyar kididigar lissafin gine- gine da Digirin na biyu akan Gine-gine da kuwa wani digrin na biyu kan Cimma Maradun Karni da kuma Digiri da sauran diploma na fannoni daban daban har da ta bangaren ilmi.
Dakta Memba ne a kungiyar kula da kididdigar gine-gine ya kuma yi rubuce- rubuce na ilmi da dama, wasu an buga wasu ba a buga ba, ya kuma samu kambin girmamawa da dama, a ciki da wajen kasar nan.
A ganin siyasa ya rike muka mai tun daga kansila har zuwa kantoma na karamar hukumar malumfashi. Ya rike shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa na jahar katsina.yayi aiki a kwamitoci daban daban a jahar katsina da kasa baki daya
Dakta Aminu Garba Waziri ya kasance Mai sha’awar bincike-bincike da karance-karance da kuma san tafiye tafiye da wasan kwallon dawaki, polo. Yana da mata da yara.
Katsina city news
Www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
Www.taskarlabarai.com
The links news
Www.thelinksnews.com