TARIHIN JAMI AR IHERIS TA KASAR TOGO..
…..Wadda ta karrama dakta Mustafa inuwa da uzee Usman
Zainab Abdullahi
@ katsina city news
Kasar Togo,kasa ce da ke yammacin afrika , babban birnin ta shine lome.
A kidayar shekarar 2018 yawan mutanen ta su milyan bakwai ne da doriya.
Kashi 46 na mutanenta kiristoci ne, sai kashi 36 masu bin addinin gargajiya.kashi shidda kuma Muslumai.
Wadansu yan Najeriya yan asalin Kano sune,suka kafa jami ar iheris a kasar .binciken katsina city news a hukumar rijistar kamfanoni a Najeriya ya nuna
Wadanda suka kafa kamfanin da ya mallaki jami ar sunansu, Baffa Bala da kuma Baffa Ahmad da baffa I bashir.duk adireshin da akayi amfani dasu na cikin birnin Kano ne.a jahar Kano.
Jami ar ta Nemi Amincewar gwamnatin Najeriya a matsayin jami ar kasar waje a cikin watan Nawumba na shekarar 2020.a takardun da muka samu na jami ar.
A kasar Togo akwai jami oi guda Goma. Iheris na daya daga cikin su.
Da yake shekarar jami ar daya kenan da budewa, jami ar bata taba yaye dalibi ko daya ba.amma ta dau dalibai a shekarar 2020 da kuma 2021.
A ranar 30 ga watan oktoba 2021 sukayi bukin daukar sabbin dalibai.karo na biyu .inda sukayi a wani dakin taro mai daukar mutane dari da hamsin.
A bukin sun hada, harda bada kyaututtuka da kuma bayar da digrin girmamawa ga wasu mutane cikin su har da Alhaji Mustafa Muhammad inuwa daga katsina. Da wani Dan wasan hausa daga Kano.mai lakabin uzee Usman
Jami ar yanzu tana da dalibai dari biyu da yan kai .kuma yanzu take gogoriyar neman karbuwa da kuma dalibai daga Najeriya da sauran kasashe.
Katsina city news
Www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
Www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
Www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245