Tarihin Marigayi Khalifa Isyaka Rabi’u
- Bayanai sun nuna cewa an haifi marigayin ne a 1928
- Ya yi karatun AlKur’ani da na addinin musulunci a birnin Kano
- Kafin daga bisani a tura shi birnin Maiduguri na jihar Borno domin kara karatu
- Ya koma Kano inda ya ci gaba da koyar da karatun Kur’ani da na addini.
- Daga baya ne kuma ya fara harkokin kasuwanci inda ya kafa kamfanin Isyaka Rabiu & Sons
- Ya yi fice matuka a fagen kasuwanci da na karatun Alkur’ani
- Daga bisa ni an nada shi Khalifan Darikar Tijjani a Najeriya
- Harkokin kasuwancin da ‘ya’yansa suka gada kuma suka ci gaba da samun daukaka a kai