TARIHIN QS ALHAJI MANNIR YAKUBU.

0

TARIHIN QS ALHAJI MANNIR YAKUBU. …mataimakin gwamnan katsina .
……Mai neman APC ta tsayar dashi takarar gwamna katsina.
Daga
Bashir Suleiman
@ katsina city news

An haifi Alhaji Mannir Yakubu a 15 ga watan Ogasta na shekarar 1954, ya fito ne daga tsatson Shehin Malamin nan, Malam Ladan dake tsuhuwar Kasuwa Katsina.

Mahaifin Alhaji Mannir, wato Alhaji Yakubu shi ne da na hudu a cikin zuri’ar Alkalin Kankia Alhaji Abdulbaki, kuma shi ne ya kirkiri cobiyar kasuwanci ta Katsina, wato, (Katsina Chamber of commerce), ya kuma kasance, dan’uwa ga Alhaji Mustapha tsohon Alkalin Alkalai, na lokacin Sarkin Katsina, Muhammadu Dikko.

Hausawa na cewa ” Barewa bata gudu, danta ya yi rairafe” don haka, Alhaji Mannir ya kara martaba darajar gidansu, kan batun ilmi, domin ya fara karatun addini tun yana dan shekara uku, ya yi sauka yana da shekara 11. Ya kuma shiga firamare ta Rafindadi a shekarar 1961 inda ya kammala a 1967 ya wuce shahararrar makarantar nan, ta Kwalejin Barewa dake Zaria, a shekarar 1968, inda ya kammala da sakamakon karatu Mai daraja ta 1 daga hukumar tsara jarabawa ta Afrika, wanda hakan ya ba shi damar shiga jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria, a Shekarar 1974 inda ya karance harkar safiyo ya kuma kammala da sakamako mafi inganci, wato second Class Upper, ta dalilin haka ne ya karbi kambin girmamawa na dalibi mafi hazaka na masu karatar ilmin safiyo.

Alhaji Mannir Yakubu, ya yi gwagwarmaya sosai a harkokin aikace- aikacensa da kuma harkokin siyasa. Don tun bayan kammala a katunsa a shekarar 1977 ya tafi bautar kasa a jihar Imo a shekarar 1978 inda ya yi aiki a ma’aikata gidaje ta jihar, kuma a sashen kula da safiyon gidaje.

A watan Ogastan 1978 ya yi aiki a matsayin Babban jami’in safiyo a hukumar kula da harkokin gine – gine, har zuwa watan goma ba shekarar 1979. Haka ma, a lokacin gwamnatin PRP ta Balarabe Musa, ya yi aiki a Ofishin Matakin Gwamna ba lokacin a matsayi sakatare na Abba Musa Rimi, kuma a lokaci guda shi ne, mai bada shawara kan batun kwagiloli.

A shekarar 1980, aka mayar da shi ma’aikatar ayyuka ta jihar Kaduna, a sashen kula da kididigar gine – gine a matsayin Babban jami’in sashen. A shekarar 1982 ya samu babbar Difloma a makarantar kula da harkokin kididigar gine – gine ta kasa, wanda hakan ta ba shi damar zama cikakken memba na kungiyar masana harkar kididdigar gine – gine ta kasa.

See also  IPI NIGERIA CONDEMNS ZAMFARA GOVERNMENT’S SHUTDOWN OF MEDIA ORGANISATIONS

A lokacin aikin da hukumar ayyuka da gidaje ta jihar Kaduna ya kawo cigaba da dama da ingantattun tsare tsare. Bayan kammaluwar wa’adin gwamnatin PRP a shekarar 1983, ya aje aiki don kashin kansa.

Ya shiga harkokin kwagiloli da duba ayyuka, inda suka samar da kamfani, inda suka yi ayyuka da dama, a kasar nan, kamar a hukumar NECOM, sake Marina Legos da Sakatariya ta NUC dake Abuja da Ma’aikatar Sufuri da NACB da sauransu, ko baya ga haka ya yi rike matsayi da dama na kula harkokin ayyukan gine – gine har da na hukumar PTF da ta aiwatar a yankin Arewa maso Gabas na kasar nan.

Kasantuwar Alhaji Mannir Yakubu yana tare da makarantar kididdiga ta kasa, ta ba shi, damar kasancewa mai kula da harkokin jarabawa na waje, na Kwalejin Kimiyya da fasaha ta kauran Namoda, dake Zamfara, tun daga shekarar 1985 har zuwa 1995 ko baya ga haka ya yi aikace- aikacen da dama a hukunomin makarantu na jihohi da kwamnatin tarayya, ya kuma kasance memba a hukumar gudanarwa na jami’ar Kimiyya dake Yola.

A harkokin siyasa Alhaji Mannir Yakubu, ya taba tsaya takarar Danmajalisar Dattawa a shekarar 2003 da 2007 a karkashin tutar jam’iyyar ANPP, yana cikin tushewa mafarin dawa, da suka kafa Jam’iyyar CPC har kuma ya yi mata takarar Gwamnan a shekarar 2011.

Ya kuma kasance Matamakin Gwamnan Katsina, a shekarar 2015 na Gwamnan Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari, inda ya yi aiki tukuro karkashin maigidan nasa, tare da jajircewa da biyaye da ta Kai su ga kara samun nasara, a wa’adin mulki na biyu na shekarar 2019, wanda aka rantsar da su a 29 ga watan mayu.
Ya rike ma aikatar gona ta jahar katsina tsawon shekaru bakwai. Ya kuma Rike kwamitoci daban wand yayi aiki tukuru.daga cikin su akwai kwamitin tallafin annobar korona da ta tallafawa wadanda bala in ta addaci ya shafa da sauran su.
Yanzu haka yana neman jam iyyar APC ta bashi tikitin takarar gwamnan katsina a zaben 2023
Alhaji Mannir Yakubu mutum ne nagartacce, kuma magidanci dake da mata da yara.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779.08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here