Tarihin Rayuwar Sheikh Jafar Mahmud Adam Kano

0

Kafin rasuwarsa, Malam ya fara gagarumin aikin Rubuce tafsirinsa a harshen Hausa a karkashin wannan cibiya (Sheikh Ja’afar Islamic Documentation Centre).

Marigayi Sheikh Ja’afar Mahmoud Adam ya rasu ranar juma’a 26/Rabii’u Awwal/1428
(13/04/2007) sakamakon harin da wadansu’yan ta’adda suka kai masa, a daidai lokacin da
Yake jagorantar sallar asuba a MasallacinJuma’a na dorayi. Dake Kano,  Ya rasu ya bar Mata biyu, da ‘yaya shida, yayin da aka haifa masa ta bakwai kwanaki 58 daidai bayan aiwatar da wannan kisan gilla a kansa.

Dubun-dubatar mutane ne daga ko’inacikin kasar nan suka Halarci Jana’ Izarsa,
kuma an binne shi ne a makabartar Dorayi. Allah ya ji kan sa ya Gafarta Masa, yayi
mas a tagomashi da gidan aljanna.Amin
.
ALLAH YAJIKAÑ MUSULMAI ÑA DUÑIYA BAKI DAYA AMIN

Shaikh Ja’afarMahmoud Adam a garin Daura, a shekarata 1962 (ko da yake wani lokacin  Yakan CE1964). Marigayi Sheikh Ja’afar ya fara karatunsana allo a gidansu, a Mijin Wurin Yayarsa, Mallam Haruna, wanda kuma dan uwansu ne najini. Daga nan kuma sai aka mayar da shiwajen wani Malam Umaru a wani gari wai shi Koza,

Kimanin kilomita 9 a arewa da Daura,wanda shi ma akwai dangantaka ta jini a tsakanin su, wanda kuma shi nemusabbabin zuwansa Kano. Bayan sun zo Kano ne tare da wannan malami nasa, a shekara ta 1971 (ko 1972), sai suka zauna a makarantar Malam Abdullahi, Wanda asalinsa mutumin jamhuriyar Nijar ne, amma yake zaune a unguwar Fagge a Kano.

Tun kafin zuwansu Kano, tuni marigayi Sheikh Ja’afar ya riga ya fara haddar Alkur’ani mai girma, wanda ya kammala a shekara ta 1978.Bayan da Malam ya kammala haddar Alkur’ani mai girma, kasancewarsa maisha’awar ilimi, sai ya shiga makarantu biyu alokaci daya a shekara ta 1980 Ya shiga makarantar koyon Larabci tamutanen kasar Misra a cibiyar yada Al ‘ Adun Rude Misra, Egyptian Cultural Centre), sannankuma ya shiga makarantar manya da ba suyi boko ba ta Masallaci Adult Evening Classes,

Tunda a lokacin shekarunsa sun wuce shekaruna primary, amma duk da haka a
wannan lokaci shi ne mafi kankanta a ajinsu. Haka ya rika yin wannan karatu guda biyu: Waccan makarantar ya je ta da Daddare Bayan Sallar isha ‘ in, da waccan kuma ta koyo harshen larabcin da yamma.

Ya kammala wadannan makarantu a Shekara ta 1983 Wannan kuma shi ya ba shi damar shiga makarantar GATC Gwale a shekara ta 1984, kum a ya kammala a shekara ta 1988.
A shekara ta 1989, ya sami gurbin karatu ajami’ar musulunci ta Madinah, a inda ya
karanta Ilimin Tafsi wanda kuma ya kammala a Shekara ta 1993.

See also  Za a sake tantance masu cin moriyar shirin N-Power da aka tsallake wajen biya

Sannan kuma Sheikh Ja’afar ya samidamar Kammala karatunsa na digiri na biyu
(Masters) a Jami’ar Kasa-Da-Kasa Ta Afrika da Take Khartoum, Sudan. Sannan kuma, kafin Rasuwarsa, ya yi kokari wajen kammala karatunsa na digiri na uku, wato digiri na digirgir (Phd), a Jami ‘ ar Usman dan Fodiyo da take Sokoto.

Daga cikin malamansa na ilimi, akwai malaminsa na farko, mutumin kasar Masar, Sheikh Abdul-Aziz Ali al- Mustafa, da kuma Malam Nuhu a unguwar dandago, Kano Wanda malam ya karanci ilimi fikihun malikiyya Da wadansu  Littattafai na hadisi a gurinsa, da Kuma Malam Muhammad Shehu, mutuminLokoja, wanda Malam ya karanci nahawu dasarfu da balaga da adab a wajensa.

Akwai kuma Jibrin Abubakar Sheikh Limamin Masallacin Juma’a BUK, akwai
kuma Dr. Ahmad Muhammad Ibrahim shima na jami’ar Bayero ta Kano. Daga cikin
malamansa na jami’a kuma, akwai Sheikh Abdurrafi ‘ u da Dr.. Khalid Assabt.

Daga cikin karatuttukan da malam ya karantar da su, sun hada da tafsirin Alkur’ani mai Girma, kitabuttauhiid, Umdatul Ahkaam, ARB’UNAHadiith, Kashfusshubuhaat, Bulugul Maraam, Riyaadussalihiin, Siiratun Nabawiy, Ahkaamul Janaa’iz, Siffatus salaatun nabiiy.

Wasu daga cikin daliban malam sun hadada Malam Rabi’u Umar R/lemo da Malam Sani Abdullahi Alhamidi dorayi da Mallam Abdullah Usman da Malam Usman Sani Haruna da Malam Ibrahim Abdullahi Sani Da Malam Yunus Ali Muhammad da Dr. Salisu Shehu da Malam Shehu Hamisu Kura da malam anas Muhammad Madabo.

Kafin rasuwarsa, Malam ya fara gagarumin aikin Rubuce tafsirinsa a harshen Hausa a karkashin wannan cibiya (Sheikh Ja’afar Islamic Documentation Centre).

Marigayi Sheikh Ja’afar Mahmoud Adamya rasu ranar juma’a 26/Rabii’u Awwal/1428
(13/04/2007) sakamakon harin da wadansu’yan ta’adda suka kai masa, a daidai lokacin da
Yake jagorantar sallar asuba a MasallacinJuma’a na dorayi. Dake Kano,  Ya rasu ya bar Mata biyu, da ‘yaya shida, yayin da aka haifa masa ta bakwai kwanaki 58 daidai bayan aiwatar da wannan kisan gilla a kansa.

Dubun-dubatar mutane ne daga ko’inacikin kasar nan suka Halarci Jana’ Izarsa,
kuma an binne shi ne a makabartar Dorayi.

Allah ya ji kan sa ya Gafarta Masa, yayimasa tagomashi da gidan aljanna.
Amin
.
ALLAH YAJIKAÑ MUSULMAI ÑA DUÑIYA BAKI DAYA AMIN

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here