TARON KASUWANCI A KASAR SAUDIYYA

0

TARON KASUWANCI A KASAR SAUDIYYA….
….Alhaji Dahiru mangal yana cikin tawagar shugaban kasa Buhari.
Muazu hassan
@ katsina city news
Hamshakin attajirin nan Dan katsina Alhaji Dahiru bara u mangal yana cikin tawagar yan kasuwa daga Najeriya da suka rufa ma shugaban kasa Muhammadu Buhari baya zuwa wajen taron kasuwanci da kasar saudiyya ta shirya a birnin Riyadh.
Taron ya gayyaci shugabannin kasashen duniya daban daban ya kuma gayyaci manyan attijarai da fadin duniya.
Taron Wanda aka fara talata 26/10/2021 za a karkare alhamis 28/10/2021.wanda shugaban kasa Buhari zai gabatar da hajjin Ummara ranar jumma a kafin ya dawo Najeriya..
Fadar shugaban kasa ta gayyaci Alhaji Dahiru mangal ya zama daya daga cikin yan kasuwa daga Najeriya da zasu halarci taron.kuma ya tafi ne a cikin jirgin fadar shugaban kasa.
Alhaji Dahiru mangal shine ya mallaki kamfanin Jiragen sama mai jigilar Alhazai mafi karfi a yammacin afrika .
Yana kuma da hannun jari a kamfanin mai na Owando.da kamfanin casar shinkafa da takin zamani.
Kamfanin sa na Afdin yana tafiyar da manyan ayyuka a fadin kasar nan a gwamnatin jihohi Dana tarayya.
Mangal na da katafaren gine gine na haya a Abuja da wasu jihohin kasar nan.
Attajiri ne, da dubbai ke cin abinci karkashin sa, ta aiki a kamfanonin sa.
Katsina city news
Www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
Www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
Www.thelinksnews.com
07043777779 081377777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here