Taron PDP ne ya firgita APC ta tsayar da buhari takara- Sule Lamido

0

Daga Rahoton BBC

Tsohon gwamnman jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya ce taron da PDP ta yi a jihohin Jigawa da Katsina ne ya firgita jam’iyyar APC har shugabannin jam’iyyar suka roki Shugaba Muhammadu Buhari ya fito ya ayyana cewa zai sake yin takara a karo na biyu.

A wata hira da ya yi da BBC Sule Lamido ya ce : ”Ai taron da aka yi a Jigawa da na Katsina shi ya firgita su, suka ce ranka ya dade gara fa ka zo, domin yadda aka yi taron nan na Jigawa da Katsina, idan ba ka zo ka ce za ka yi takara ba mun shiga uku…”

See also  MATASA DA SANA'ARSU

Tsohon gwamnan ya kara da cewa APC da Buharin sun yi hakan ne domin su samu dan hutu na ”Tsunamin” da PDP ta yi a jihohin biyu a tarukanta.

Ya ce sai ma jam’iyyar tasu ta yi irin taron a Sokoto, Kaduna da Kebbi kafin kuma ta yi na Abuja lokacin da hankalin shugaban da jam’iyyarsa za su fi tashi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here