TATTAKIN KATSINA ZUWA KANO: ‘YAN JARIDA SUN RABE TSABA DA TSAKUWA

0

TATTAKIN KATSINA ZUWA KANO: ‘YAN JARIDA SUN RABE TSABA DA TSAKUWA ~~~INJI DANJUMA KATSINA

Mawallafin jaridun Taskar Labarai da The Links News ya bayyana cewa, tattakin da wani yayi ikirarin yayi daga Katsina zuwa Kano don Ganduje, ‘yan jaridu sun rarrabe tsaba da tsakuwa, in da duk jaridun suka kauracema labarin ban da guda daya da ta yi labarai biyu, sai kuma gidan rediyon jiha da yayi labarin saboda mataimakin gwamna.

Danjuma na magana ne, da wasu matasa da suka kawo masa ziyara a yau don neman shawarar kafa wani gidan rediyo da talabijin a bisa yanar gizo.

Danjuma ya karfafa masu gwaiwa da cewa su kuma nemi ilmin abin da suke son su shiga, domin da ilmi ake nasara ga duk abin da ka sanya a gaba. Yace in ba ilmi ana iya baka shawara ka dauka zaginka ake yi.

A nan ne ya bada misali da mai tattaki yace da ya fara ya jawo wasu marubutu a yanar gizo don su tallata kuma yayi fatan ‘yan jaridu ma su shigo hidimar ta sa tun da yayi hakan, ya jawo ana iya nazari akan abin da yake.

Danjuma yace mu a Taskar Labarai, labarai uku kadai muka yi akan tattakin daya akan shi tattakin biyu kuma akan wani Dan majalisar jiha, da yayi magana a fadar gwamnatin Kano.

Yace mun yi niyyar rubutu ne, don bayyanar da fahimtar mu da matsayarmu a kan ikirarin na takawa daga Katsina zuwa Kano. Ya cigaba da cewa a fadar matsaya da gaskiya babu ga babba ko yaro. Yace “”na taso a gida mai tsauri naje makarantar kwana inda wanda ya fika da aji daya, sai ya dawwara ka, na kuma rayu gaban mutane, wadanda basu san wasa ba.””

See also  2023: Doguwa ya zargi mataimakin dan takarar gwamnan Kano na APC da yiwa Atiku aiki

Yace in kaga yaro na tada jijiyar wuya don an fada masa gaskiya to binciki tarbiyarsa ko ya bijirewa tarbiyar da ya samu.. Ko kuma yana bayyana abin da ya tashi ya gani kenan.
Daya daga cikin masu neman shawarar yace masu tattakin sun ce sun yi nasara.

Danjuma yace kwarai kuwa sun yi nasara irin wadda suka je nema, an sauke su a otal sun rika cin abin da suke so ( sama da miliyan daya a kwanakin da sukayi) a ranar karshe an masu liyafa mai kyau, an kuma yi masu kyauta, don haka sun yi nasarar abin da suka je nema.

Wasu kuma sun yi nasarar bayyana matsayinsu akan tattaki kuma al’umma ta fahimta.

Danjuma yace, gwamnan Kano Ganduje yaki ganin mai tattakin ne da kuma tawagar sa, saboda wasu bayanan sirri da ya samu a matsayinshi na mai ilmi kuma gogaggen dan siyasa, yace ganin su akwai matsala.

Danjuma yace abokan mu a cikin gwamnatin Kano sun fada mana cewa Ganduje ya tambaya mai tattakin su nawa suka zo aka ce sun kusa arba’in, yace wadanda suka rako shi ne ko wadanda suka biyo cin arziki? aka yi dariya da ga nan labarin ya canza, yawan tawagar mai tattaki ya rage mashi sa’a sosai.

Danjuma ya jaddada wa matasan su nemi ilmin aikin gadan-gadan kuma kullum su rika sabunta ilmin nasu, yace tun da nake shiga aji shekaru talatin da suka wuce ban taba barin shekara ta cika ba, face akwai kwas din da nake koyo ko yanzu ni dalibi dan aji daya ne a wani kwas a jami’ar Al-Qalam.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here