TSOHON MINISTAN ISRA’ILA WANDA YA YI WA IRAN LEKEN ASIRI YANA NIJERIYA A BOYE

0

TSOHON MINISTAN ISRA’ILA WANDA YA YI WA IRAN LEKEN ASIRI YANA NIJERIYA A BOYE

Daga Abdurahaman Aliyu

Hukumar Tsaro ta cikin gida a kasar Isra’ila ta bayyana tsohon Ministan kasar Segev a Matsayin mai yiwa Iran Leken Asiri.

A bayanin da ta fitar ranar Litinin ta bayyana daya daga cikin ministan kasar Wanda ya yi minista a tsakanin shekarar 1995-1996 mai suna Gonen Segev da ceqa kasar Iran ta dauke shi aiki a matsayin Dan leken asiri.

Kamar yadda kafar yada labarai ta Reuters ta rawaito sun bayyana cewa Sagev ya na zaune a Nijeriya yanzu haka, sannan yana ganawa da ambasadan Iran a Nijeriya tun a shekarar 2012.

Segey Wanda ya zauna gidan yari a shekarar 2004 a Isra’il saboda kama shi da laifin safara abubuwan da aka haramta, ya bar kasar ne a shekarar 2007.

See also  FG inaugurates N22.69bn road project in Adamawa

Tsohon Ministan ya ziyarci Iran sau biyu in da ya gana da wasu mahukuntan kasar kan abin da ya shafi bututun iskan Gas, an tabbatar da cewa ya taimaka wajen Samar da bayanai da suka shafi bututun gasa ga hukumar tsaro kasar Iran.

Tsohon ministan ya samu gindin zama ne bayan da aka hada baki da wasu ‘Yan kasar Isra’il din mazauna Iran, in da aka ambata shi a matsayin wani shaharren Dan kasuwa.

Kazalika duk wasu bayanai da suka shafi Segev a barsu ne a matsayin bayanan Sirri, kamar yadda kasar ta bukata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here