Tsufa ya zo da gardama: Kotu ta gurfanar da tsohon da ya tafka damfarar N20.7m

An gurfanar da wani dattijo Fasasi Adebambo, a gaban wata babbar kotun Legas jiya bisa laifin damfarar naira miliyan N20.7 (N20.7m)

An miƙa dattijon gaban alƙali

Adebambo, mai shekaru 84, an miƙa shi gaban alƙaliwa Akintayo Aluko tare da wani Ojobaro Kayode bisa zargin aikata zamba cikin aminci. Jaridar The Nation ta rahoto

Sashin ‘yan sanda na Police Special Fraud Unit (PSFU), wanda ya miƙa waɗanda ake zargin, ya tuhume su da cewa sun amshi kuɗaɗen ne a wajen Dr. Mbeledogu da matarsa akan cewa za su sayar musu da wani gida a yankin Maryland a jihar Legas.

Mai shigar da ƙara na PSFU, Henry Obiaze, ya faɗawa kotu cewa waɗanda ake zargin sun tafka wannan aika-aikar ne tsakanin watan Janairu da Fabrairun 2020.

See also  SHARI'AR SHAIKH ZAKZAKY

Ya bayyanawa kotu cewa laifukan da su ka aikata sun saɓawa sashin doka na 8 (a) da 1(1)(a) na hana aikata damfara da sauran laifuka makamantan su na shekarar 2006. Sannan kuma abin hukuntawa ne a sashi na 3 na cikin dokar.

Sun ƙi amsa aikata laifin

Waɗanda ake zargin sun musanta aikata laifukan da ake zargin su da aikatawa.

Bayan sun musanta aikata laifukan, mai shigar da ƙara ya nemi kotu da ta sanya ranar fara shari’a sannan ya buƙaci kotu da ta sakaya su a gidan gyaran hali har zuwa lokacin da za a kammala shari’ar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here