TURA TA KAI BANGO ; GA CIN KASHIN DA AKE SHUGABANNIN MU.

0

TURA TA KAI BANGO ; GA CIN KASHIN DA AKE SHUGABANNIN MU.

Ra’ayin; Comr. Mai-Iyali Katsina

Tun farko yan gwangilar kawo rikici, rudani acikin jam’iyyar PDPn jihar katsina sun rinka cewa laifin Shugaban jam’iyyar PDPn da rashin iya shugabancin sa yasa ake faduwa zaɓuka tun daga zabukan cike gurbi da akayi zuwa zubakan 2019 baki daya.
A nasu tunanin da hangen da ba Hon.Salisu Yusuf majigiri bane shugaban jam’iyyar PDP da jam’iyyar PDPn lashe wadannan zaɓukan da aka gudanar, kuma da yanzu jihar Katsina PDPn ce ke mulkin ta daga sama har ƙasa.

Duk al’amari idan ana so yin adalchi aza shi ake bisa mizanin adalchi da sikelin hankali, sai ma’abota adalchi da hankali suyi alƙalanci su fitar da gaskiya, don haka yau zamu ɗaura shugabancin da kokarin Hon.Salisu Majigiri bisa sikeli mu kuma yi duba da yadda sauran jihohin Arewa suma suke tafiyar da jam’iyyar PDP kuma suma basu yi nasara ba, daga nan sai mu gane shin laifin Hon. Salisu Majigiri ne ko kuma dai yanayin SAK ne da ƊOƊAR da ƙaddara ya kawo hakan

Kowa ƙasar nan yasan Sule Lamido a duniyar siyasa wajen dagewa da jajircewa, amma shima tun daga 2015 har akayi babban zabe bai ci kujera ko ɗaya ba, duk kuma wata hidimtawa da zaiyi ma PDP yayi mata, amma Allah bai kawo nasara ba, ƙarshe aka samu masu hali irin naku suka ja daga suka ce a ƙwace jamiyya hannun Lamido a basu, ƙarshe suka ji kunya aka kore su. Shima Sule Lamido kuna nufin bai iya bane shiyasa hakan ta faru?.

A jihar Gombe, PDP tana kan mulki, gwamnan jihar ya nemi Sanata shi kuma Sanatan ya nemi gwamna, amma haka suka zo su duka suka faɗi, PDP bata ci zaɓen shugaban ƙasa ba, bata ci Sanata ko ɗaya ba, bata ci ɗan majalisar tarayya ko ɗaya ba, haka gwamna haka majalisar jiha, haka na nufin shima Dankwambo bai cancanta ba kuma baiyi abinda ya dace bane?.

Ga jihar Kebbi can, haka ta faru a Zamfara saidai kotu ta kwace taba su, Sokoto ma da kyar PDP ta sha da kujerar gwamna babu Sanata ko ɗaya, jihar Borno PDP bata da kujera ko ɗaya haka ma Yobe. Bauchi ma da ƙyar muka tsira da kujerar gwamna, amma a majalisar jiha APC keda rinjaye. Yanzu sai ku kalli duk shuwagabannin jam’iyyu na jihohin nan kuce basu cancanta ba, basu yi abinda ya dace ba, anya kun zama adalai?

See also  Zamu Kai Ƙara Kotu Kan Magudin Zaɓe Da Akai Mana -- PDP

A siyasa wayasan Lawal Rufa’i Safana kuma mutanen nan basuda niyyar sasanci ai tun kafin congress kungiyar tasu sunzo an fara zama dasu sasanci sun kawo bukatunsu suna son kujerar mataimakin chairman shi Lawal Rufai da PRO, Farko an fara zama dasu suka koma suka rika cudanya da gwamnatin Masari hadda neman kwagiloli Kuma suka chigaba da batancinsu, To ta’ina zakayi sasanci da wadannan, Masu cewa ayi sasanci tayaya mutum ka fara magana dashi ya kauce ya koma batannci kace ya shirya ayi sasanci,

Ai ina ganin duk wani dan PDP na hakika yasan anyi hakuri dasu, yanzu kuma bayan kararraki guda shidda da suka kai kotu, bisa zarge-zarge daban-daban duk mai kaunar PDP dole ya yarda, hakurin koma cutar da jammiyya ne, Kuma wannan na kara tabbatarda niyarsu ta kawo rikici, rudani acikin PDP katsina. Shi dai mulki Allah ke badashi ga wanda yaso da lokacin da yaso, bamu jahiltar kanmu da neman mulki ta ko wane hali,

Masu koma alakanta Lawal Rufai safana cikin yaran marigayi yar’adua, yaushe ya shigo PDP dazai zama yaron yar’adua, Shi adawa yayi dashi Domin APP yake sai bayan 2003 yana director, bayan yaga PDP nada karfin chin zabe amatsayinsa na ma’aikacin gwamnati ya shigo PDP, to wannan shine yaron yar’adua, shikenan sai mu bashi shugabancin PDP tun shigowar shi PDP, Jam’iyyar PDP bata taba cin safana local government tashi ba kuma adalilinsa PDP ta fara rasa manyan diyanta a Safana, gaskiya bazamu ba wannan rikon jammiyyar mu ba Mu masoya PDP na hakika

Kuma masu kiran kansu yaran Mallam Ummaru, it’s on record Masari shiya shugabanci arna akan Mallam Ummaru yar’adua ya sauka daga shugaban kasa yaba arne Goodluck, lokacinda yake kwance gadon asibiti, To masu tarayya da wannan sune masoya Mallam Ummaru, kamar yadda na fada a baya,mu daina yaudarar kanmu, duk masoyin Mallam Ummaru yar’adua bazaiyi tarayya da Masari ba saboda bayyanan nan labari ne Masari baya kaunar Mallam Ummaru yar’adua

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here